1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Warware rikicin Libiya ta hanyar diplomasiya

August 10, 2011

Amirka ta tura wasu manyan jami'anta zuwa Afirka domin shiga su tattaunawa akan rikicin Libiya da kuma yiwuwar saukar Gadafi daga karagar mulki

Muammar Gaddafi akan hanyarsa ta ganawa da wata tawwagar AUHoto: dapd

Manyan jami'an Amirka na ziyartar wasu ƙasashen Afirka a matsayin yanki na ƙokarin shawo kan Shugaba Muammar Gaddafi da ya sauka daga karagar mulki. Wasu ƙasashen na Afirka na shan suka ne bisa jan ƙafa da suke yi wajen yin kira ga shugaban na Libiya da ya sauka daga karagar mulkin da kuma yin suka ga hare-haren NATO -abin da aka danganta da taimakon kuɗi da suke samu daga gwamnatin Gaddafi.

Tuni Gene Cretz, jakadan Amirka a Libiya da ya fice daga ƙasar kafin Gaddafi ya fara ɗaukar matakin murƙushe 'yan adawa a watan Fabarairu da babban mataimakin sakataren harkokin wajen Amirka, Donald Yamamoto suka isa birnin Addis Ababa, helkawatar Ƙungiyar Gamayyar Afirka(AU) inda za su gana da ƙasashe mambobin ƙungiyar domin tattatunawa rikicin Libiya da kuma bukatar saukar Gaddafi daga karagar mulki. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amirka, Mark Toner ya ce tuni jami'an suka gana da Fraimnista Meles Zenawi suna kuma shirin ganawa da magakujerar ƙungiyar ta AU, Jean Ping.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu