1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasan al'adar Tabastaka a kasar Nijar

April 23, 2025

A birnin Maradi na jamhuriyar Niger an bude gasar wasan festival na tabastaka karo na takwas karkashin jagorancin ministan matasa da raya al'adu

Bikin al'adar gargajiya a Nijar
Hoto: Harandane Dicko

Ministan matasa da wasanin motsa jiki da raya ala'adu Kanal Manjo Abdramane Amadu shi ya bude bikin wasannin karo na takwas wanda jihar Maradi ta karbar bakuncinsa a bana. Dukanin jahohi takwas na kasar sun amsa goron gayyata na wannan kasaitaccen bikin raya al'adar da aka gada tun Iyaye da kakanni.

Gwamnan jihar Maradi wanda shi ne mai masaukin baki, ya ce tabastaka baban arziki ne saboda haka kowa ya bada gudunmawa don kara dabakata al'adar.

To ko wane irin tasiri al'ada ke da shi wurin tabbatar da zaman lafiya a Nijar? Dr Nuhu Salihu Jangorzo malamin Jami'a, ya bada lacca kan asaili da tasirin wannan al'ada

iahar Maradi mai Katsinawa da Gobirawa a cewar Shaibu Begu madubi ce a game da wasan tabastaka 

Tuni dai 'yan wasa suka soma baje kolinsu gaban 'yan kallo.