Makomar Najeriya a wasannin Afirka
December 1, 2025
A kwanan nan ne aka kammala wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya wanda manyan kasashe suka gaza samun sukunin tsallake siradi, irin su Kamaru da Najeriya, wannan ta sa aka shiga muhawara a Najeriya, sakamakon karatowar gasar cin kofin nahiyar Afirka wato AFCON, wanda za a gudanar a cikin wannan wata na Disamba a kasar Maroko.
Yanayin da Najeriya ta samu kanta
Shin ko Super Eagles din za ta taka rawar gani don huce haushin rashin waccan gurbi na kofin duniya? Tsohon ɗan wasan Najeriya Garba Lawal, ya bayyana cewa babban kalubalen Eagles shi ne karancin kishi da rashin sanin darajar Kungiyar ta kasa daga wasu ‘yanwasa ke yi. Duk da wadannan kalubale, masoya da masana suna fatan Super Eagles za su shirya sosai, su kuma dawo da farin ciki a zukatan ‘yan Najeriya a gasar da za ta gudana a Maroko.
Samun rauni lokacin wasa
Fitacciyar 'yar wasan kwallon kafar kasar Spain Aitana Bonmati ta samu karaya a kafarta, a daidai lokacin daukar atisaye a birnin Madrid ranar Lahadi, gabanin karawar da kasarta za ta yi da Jamus, a wasan karshe zagaye na biyu na neman lashe gasar kwallon kafar mata ta nahiyar Turai.
Bonmati ita ce 'yar wasan Spain da ta taba lashe gwarzuwar shekara wato Ballon d'Or har sau uku, inda yanzu za ta koma kungiyarta ta Barcelona domin fara jinya.
Kwallon kwando
A wasannin share fagen tunkarar gasar kwallon kwando ta duniya, ta shekarar 2027 da za a gudanar a kasar Qatar, Burtaniya ta farfado daga kashin da ta sha har gida birnin London a hannun Lithuania da ci 89-88, inda ta lallasa mai masaukin bakinta Iceland da ci 90-82.
Kasashe 31 za su samu damar halartar gasar, sai ta 32 mai masaukin baki Qatar.
A gasar kwallon kwandon Amurka, Atlanta Hawks ta samu nasarar casa Philadelphia 76ers da maki 142-134. 'Dan wasanta Jalen Johnson shi kadai ya samar wa kungiyar maki 41.
A wani wasan kuma fitaccen 'dan wasan nan LeBron James bai samu zarafin buga wasan da kungiyarsa Los Angeles Lakers' ta doke da Orleans Pelicans da maki 133-121, sakamakon raunin da yake fama da shi a kafarsa ta hau.