1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniFaransa

Wasanni: 05.08.2024

Suleiman Babayo AH
August 5, 2024

((Shirin ya mayar da hankali game da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya da ke gudana a birnin Paris na kasar Faransa,

Hoto: Matthias Schrader/AP/picture alliance

Kasashen duniya na ci gaba da fafatawa a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya Olympics domin samun lambobi. Kaylia Nemour daga kasar Aljeriya ta zama ta farko daga nahiyar Afirka da ta samu lambar zinaye a tsallen juyawa ta karfe a gasar na guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya. Ita dai Kaylia Nemour 'yar shekaru 17 da haihuwa ta samu nasarra a wannan Lahadi da ta gabata. Yayin da tafiya ta yi nisa a gasar Olympics da kasar Faransa ta karbi bakuncinta ta shekara ta 2024 a babban birnin kasar Paris, kalilan daga cikin kasashen Afirka sun lashe kyautar zinare da azurfa a matakai dabam-dabam.

Hoto: Matthias Schrader/AP/picture alliance

A teburin na wasannin na Olympics kasar China take kan gaba wajen samun lambobi, yayin da Amirka ta yi hubbasa ta shiga matsayi na biyu wajen yawan lambobin, kana mai masaukin baki kasar Faransa take matsayi na uku. Ita kuwa kasar Australiya da ta fara wasannin na guje-guje da tsalle-tsalle da kafar dama ta sauko zuwa matsayi na hudu. Sannan Birtaniya tana matsayi na biyar yayin da Jamus ta kasance a matsayi na 10 babu yabo babu fallasa.

Hoto: John Locher/AP/picture alliance

A wasan Tennins, Novak Djokovic mai shekaru 37 da haihuwa ya samu lambar zinare lokacin da ya doke Carlos Alcaraz a wasan karshe da aka kara a wannan Lahadi da ta gabta. Shi dai Djokovic daga kasar Sabiya ya samu wannan nasara mai cike da tarihi lokacin fafata wasan karshen na tennis tare da Alcaraz daga kasar Spain.

Hoto: Manu Fernandez/AP/picture alliance

Novak Djokovic ya gaza samun irin wannan nasara a wasannin Olympics hudu da suka gabata ba,da aka gudanar a Beijing da ke China, da London na Birtaniya, da birnin Rio de Janeiro na Brazil gami da na baya-baya birnin Tokyo na kasar Japan. Kuma samun wannan lamba na zinare na da tasiri ga Novak Djokovic dan kasar Sabiya da ya dade yana taka rawa a wasannin na tennis na duniya.

Hoto: James Moy/empics/picture alliance

A fagen wasan tseren motoci na Formula One, dadadden daraktan na rukunin Red Bull, Jonathan Wheatley zai sauka daga kan mukamun na Formula One zuwa karshen kakannin wasa inda a shekara mai zuwa zai kara jagorancin tawogar motocin Audi, inda zai rike mukamun nan kamfanonin biyu. Sai dai babu cikekken bayani kan yada lamarin zai kasance, abin da ake jira a gani ke nan.