1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

Wasanni: 08.07.2024

Suleiman Babayo AH
July 8, 2024

Kasashen hudu suka rage, na Spainiya, Faransa, Ingila da Netherlands a gasar neman cin kofin kasashen Turai da Jamus ke daukan nauyi.

Hoto: Friso Gentsch/dpa/picture alliance

Talata ake shiga matakin wasan kusa da na karshe a wasan neman cin kofin kasashen Turai da ke gudana a Jamus, kuma ita kanta Jamus mai masaukin baki tana cikin kasashen da aka cire a wasan kusa da na kusa da na karshe, lokacin karawa da kasar Spaniya, inda aka samu galaba kan Jamus a mintoci karshe na karin lokacin bayan tashi 1 da 1. Kuma karshen Spaniya ta yi galaba kan Jamus da ci 2 da 1. Ingila tana cikin kasashe hudu da suka kai wasan kusa da na karshe bayan doke Switzerland a bugun da kai sai mai tsaron gida sakamakon tashi daga wasa 1 da 1:  "Mun yi iya kokarinmun, mun ga yadda suke wasa da kyau domin haka tilas muka sauya dabara"

Gasar tseren motoci na Formula One

Hoto: James Moy/empics/picture alliance

A tseren motoci na Formula One, Lando Norris ya daura laifi zama a matsayi na uku kansa wanda ya kasance karkashin tawagar McLaren lokacin teren da aka yi a wannan Lahadi da ta gabata a Birtaniya, inda ya nuna takaicin rashin samun nasarar zama na farko a tseren, da shi ma kwarzo Max Verstappen na tawogar Red Bull ya kasance a matsayi na biyu, inda Lewis Hamilton yake matsayi na farko a tawogar Mercedes.

Shin gasar Olympics na duniya

Hoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

Yayin da ake shirin fara wasan guje-guje da tsalle-tsalle na duniya Oliympics da birnin Paris na Faransa zai dauki nauyi daga ranar 26 ga wannan wata na Yuli zuwa ranar 11 ga watan gobe na Agusta. Kasar Australia za ta tura tawagar 'yan wasan motsa jiki mafi girma a tarihin kasar da ta kunshi 'yan wasan motsa jiki 75, inda a gaba daya kasar ta Australia za ta tura wakilai 460 zuwa wannan gasa mai tasiri ta duniya. Kasar ta samu lambobin zinare 17 lokacin wasannin na guje-guje da tsalle-tsalle da aka gudanar shekaru uku da suka gabata a birnin Tokyo na kasar Japan. Haka 'yan wasan China suna ci gaba da shirye-shiryen karshe na zuwa wasannin na birnin Paris, musamma a wasan Badminzton da ake ganin kasar ta yi zarra tana kara karfafawa, da irin 'yan wasa Chen Yufei da suke ci gaba da tashe a duniya.

Rasa ba za ta halarci gasar Oliympics ba

Hoto: Thomas Bevilacqua/REUTERS

Kana ganin Rasha ba za ta tura da wakilai ba zuwa wannan wasanni na Olympics saboda matakin da aka dauka kan kasar, ya janyo ake ganin a wasu wasannin musamman na nunkaya da Rasha ta yi zarra, wasu 'yan wasan za su nuna kansu a bana. 'Yan wasa daga kasashen Rasha da Belarus za su yi gasar karkashin sunayensu amma ba kasashen da suka fito ba.