1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

WasannI : 19.08.2024

Mouhamadou Awal Balarabe AH
August 19, 2024

Akasarin lig-lig na kasashen Turai sun kaddamar da kakar wasa a karshen mako.

Hoto: David Cliff/AP/dpa/picture alliance

Manchester City ta yi abin yabo a Premier League yayin da da Real Madrid ta yi kunnen doki. Za mu ji halin da ake ciki a Jamus. A Kamaru, mahawara ta barke kan batun cancantar girmama dan wasa da ba ya rike da fasfo din kasar  bayan da gwamnati ta ba wa dan kwallon kwando na Amurka da ya taka a gasar Olympics lambar yabo. Manyan lig na kwallon kafa na nahiyar Turai sun kaddamar da kakar-wasanni a karshen mako, inda Real Madrid ta fara da kunnen doki a kasar Spain. Hasali ma dai, zakaran la Liga a bara Real Madrid ta fara kare kambunta da ci 1-1 a gidan Mallorca, inda sabon tauraronta Kylian Mbappé bai taka rawar gani. Sai dai kocinsa Carlo Ancelotti bai kwance masa mazagi a kasuwa ba, yana mai dagewa kan rashin kwazo na daukacin kungiyarsa.

Hoto: Martin Rickett/dpa/picture alliance

 

"Matsalar ba ta 'yan wasa biyu ko uku ba ce, amma matsala ce ta kungiya gaba daya, domin ko shakka babu Mallorca ta hade kai wajen taka rawar gani musamman a fannin tsaron gida. Ina ganin wannan canjaras din ya yi daidai." A nata bangaren, FC Barcelona ta samu nasarar zura kwallaye biyu daga Robert Lewandowski inda ta yi nasara da ci 2-1 tare da kauce ma tarkon da Valencia ta dana mata. Amma gabanin karawa tsakanin Atletico Madrid da Villarreal a yammacin Litinin, kungiyar Blaugranas ce ke kan gaba a teburin La Liga, inda take da maki daidai wa daida da Rayo Vallecano da Celta Vigo. A Ingila kuwa, ranar farko ta gasar Premier League ta tabbatar da nasarar Manchester City da ke rike da kambun zakara, inda a hamayyarta da Chelsea ba ta samu matsala sosai wajen samun nasara da ci 2-0 ba, sakamakon kwallayen da Kovacic da Haaland suka zura. Ko da Pep Guardiola da ke horas da Manchester City sai da ya ce Haaland dan asalin Norway ya fara farkon kakar wasa cikin karsashi.

Hoto: Revierfoto/dpa/picture alliance

 

"Ina gani kamar yana jin dadi fiye da kakar wasan da ta gabata a wannan mataki na gasar. Ina gani kamar ya fi gajiya a bara. Amma a wannan kakar, kasancewar Norway ba ta shiga gasar Euro2024 ba ya kara hutawa sosai kuma yana cikin jin dadi. Kwallon da ya zura na da kyau sosai. "Sauran kungiyoyin da su ma suka yi nasara tare da bin sahun City a saman tebur, sun hada da Arsenal da ta zo ta biyu a bara kuma ta doke takwarta Wolves da ci 2-0. Ita ma Liverpool ta shiga tsaka mai wuya a farkon wasa kafin ta samu nasara da ci 2-0 a kan Ipwish Town musamman bayan kwallon da Mohamed Salah ya ci. Amma dai akwai karon batta da za a yi a yammacin wannan Litinin tsakanin Leicester da Tottenham.

Hoto: Robert Michael/dpa/picture alliance

A Faransa kuwa, PSG ta ga da ja da janyewa, inda ta lallasa Le Havre da ci 4-1 amma da jibin goshi saboda har zuwa minti 84 da fara wasa, ana  kunnen doki 1-1 tsakanin kungoyoyin biyu kafin Ousmane Dembélé ya fara ceto Paris. A halin yanzu ma dai, PSG ba ta saman teburin gasar Ligue 1 saboda abokiyar gabanta da Marseille ta fita taka rawar gani inda ta doke Brest da ci 5-1. A sauran wasannin kuwa, Monaco ta samu nasara ci 1-0 a kan Saint-Etienne da ta dawo babban lig, yayin da Lyon ta sha kashi ci 0-3 a hannun Rennes, ita kuwa Lens ta doke Angers da ci 1-0.  A Italiya, zakaran Serie A Inter Milan ba ta yi wani abin a zo a gani ba inda ta tashi 2-2 a karawa da ta yi da Genoa. Haka ma labarin yake tsakanin AC Milan da ta tashi 2-2 daTorino. A nata bangaren, Napoli ko Naples  wacce Antonio Conte ke horarwa ta dandana kudarta da ci 0-3 a  wasan da ta yi da Hellas Verona, wacce a halin yanzu ke rike da saman teburi.

Hoto: Filippo Monteforte/AFP

A karshe a Jamus, a  daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan a yaye kallabin babban lig kwallon kafar Jamus ta Bundesliga, an fara zagayen farko na gasar kalubalen neman cin kofin kwallon kafar kasar.  A fili yake cewar zagaye na farko bai zo da wahala da yawa ba ga wadanda aka fi kyautata musu rabo ba. In ban da Bochum da sabon shiga Ratisbonne ta lallasa da ci 1-0, duk manyan kungiyoyin sun tsallake wannan zagaye na farko, inda Bayern Munich ta samu nsara a kan Ulm da ci 4-0.  Vincent Kompany, kocin Bayern Munich ya yi amfani da wannan dama wajen nuna cewar kungiyar da yake horaswa na da burin magance kura-kuran da ta take fama da su a kakar wasa da ta gabata.