Wasanni: An fitar da Masar a gasar AFCON
January 29, 2024Tafiya ta fara nisa a kokarin da kasashen Afirka ke yi na lashe gasar kofin kwallon kafar wannan nahiya da ke gudana a Côte d' Ivoire. A daidai ma lokacin da aka shiga matakin raba ni da yaro, Super Eagles ta Najeriya ta yi wajen Road da makwabciyarta Indomitables Lions ta Kamaru da ci 2-0. Ita kuwa Angola ta gasa wa Namibiya aya a hannu da ci 3-0. A nata bangaren Guinea Conakry ta doke takwarata Eqautorial Guine da ci daya mai ban haushi. Sai dai sakamakon da ya fi ba da mamaki, shi ne shammatar Masar da Kwango dimukaradiyya ta yi, inda bayan ci 1-1 da suke da shi bayan da aka yi busan karshe, wankin hula ya kai su ga bugun fenareti tara, tara, kuma a karshen mai tsaron gidan Kwango Lionel Mpasi ne ya cire wa kungiyar Leopards kitse a wuta, lamrin da ya faranta masa rai.
"Mun kalubalanci babbar kungiyar kwallon kafar Masar wacce ke da kwarewa sosai a Afirka, amma mun zo da salonmu da tsarin wasan da koci ya tsayar, wanda muka yi kokarin mutuntawa gwargwadon iko. Za mu yi kokarin fusatar da kungiyoyi masu yawa. Za mu tsaya kan abin da ya kamata mu yi".
Tuni ma dai Masar ta tattara nata ya nata ta yi gida, lamarin da wasu 'yan kasar ke dauka a matsayin wani abin kunya duba da cewa ita ce ta fi kowa yawan lashe kofin AFCON a tarihi.
Bayan ci gaba da tankade da rairaya, ciki har da karawa tsakanin Senegal da ke rike da kofin da Côte d' Ivoire mai masaukun baki, a ranar Jumma'a ne za a shiga matsakin kusa da kusa da na karshe, inda Najeriya za ta kara da Angola, yayin da Kwango dimukaradiyya za ta yi wasanta na gaba da Guinea Conakry.
Yanzu kuma sai gasar Bundesliga ta Jamus, inda aka gudanar da wasannin mako na 19. Sai dai wannan karon Bayer Leverkusen ta yi canjaras da Borussia Mönchengladbach 0-0, duk da damammakin da ta samu. Duk da cewar wannan sakamako ya haddasa takaici kocin Leverkusen Xabi Alonso ya ce bai kamata a kwallafa rai a kai ba.
"Abu ne marar dadi na rashin samun nasara, mun yi duk abin da za mu iya don samun maki uku, amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba, abu ne da ya saba faruwa. Ba mu yi wasan da ya kamata a filin kwallo ba. Ina tsammanin ba mu sarrafa wasan da kyau, amma Gladbach ta kare kanta sosai kuma a cikin tsari mai mahimmanci. Za mu yi nazarin wasan da kyau kuma zai yi mana amfani nan gaba, don sanin yadda za mu buga wasa da ire-iren wadannan kungiyoyin. Don haka muna da kyakkyawan fata."
Bayer Leverkusen na ci gaba da kasancewa a saman teburin Bundesliga da maki 49, amma a yanzu tazarar maki biyu kawai take da shi da Bayern Munich da ke biya mata baya da maki 47. Ita dai Yaya-babba ta bi Augsburg har gida kuma ta lallasa ta da ci 3-2.
A nata bangare, VfB Stuttgart ta samu nasara ci 5-2 a kan RB Leipzig, duk da cewa 'yan wasanta da yawa suna buga gasar AFCON da gasar cin kofin kwallon kafa ta Asiya. Sai dai wannan shi ne wasan farko da ta lashe a wannan shekarar ta 2024, amma kuma ita ce a matsayi na uku da maki 37. Ita kuwa RB Leipzig ta fadi zuwa matsayi na 5. Borussia Dortmund ce ta amfana sosai da wasannin inda ta samun damar zuwa matsayi na 4 bayan nasarar da ta yi a kan VfL Bochum da ci 3-1.
Kwanaki biyu bayan nasarar da ya yi a kan Novak Djokovic, dan tennis na kasar Italiya Jannik Sinner ya lashe gasar Grand Slam da ya gudana a gasar Australian Open, inda ya hambarar da Daniil Medvedev da ci 3-6, 3-6, 6-4, 6-4, 6-3. Sinner mi shekaru 22, ya zama dan wasan Italiya na uku da ya taba cin Grand Slam, inda na farko ya kasance a 1976. Wannan ne gasar maza na farko a Australian Open da aka yi ba tare da manyan ‘yan wasa irin su Novak Djokovic, Raphael Nadal da Roger Federer ba. A daidai lokacin da Federer ya yi ritaya Nadal kuma ya ji rauni, shi kuwa Djokovic aka cire shi a wasan kusa da na karshe. Shi kuwa Jannik Sinner ya samu damar cin kofin Australian Open a karon farko.
Babbar kungiyar kwallon hannu ta Faransa ta lashe gasar cin kofin Turai da ta gudana a birnin Koln na Jamus bayan ta doke Denmark da ci 33-31 bayan karin lokaci a wasan karshe. Wannan dai shi ne karo na hudu cikin tarihi da Faransa ta lashe wannan kofi, kuma na karshe ya kasance shekaru goman da suka gabata. Hasali ma wasan na karshe ya kasance maimai na gasar cin kofin duniya a bara, sai dai a wanccan karon, Faransa ta dibi kashinta a hannun Denmark. Dama dai wannan kasa ta kasance dodon Faransa inda haduwa goma duka goma, ko da shi ke a wannan karon reshen ya juye da mujiya.