1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: Rafael Nadal ya kafa tarihi

May 26, 2025

Zakaran wasan Tennis dan kasar Spain Rafael Nadal ya samu karramawa ta musamman a matsayin wanda ya kafa tarihi a gasar Tenis ta Roland-Garros, akwai sauran wasanni.

Tennis | Rafael Nadal | Zakara | Duniya | Roland-Garros
Rafael Nadal Shararren dan wasan Tennis da ya kafa tarihiHoto: Reuters/A. Kelly

Kasaitaccen biki aka yi a birnin Paris na kasar Faransa da ya samus halartar manyan 'yan wasan Tennis da suka hadar da Roger Federer da Nivak Djokovic da Andy Murray da kuma 'yan kallo sama da 15.000, domin karrama zakaran wasan Tennis din dan kasar Spaniya Rafael Nadal a matsayin wanda ya kafa tarihi a gasar Tennis ta Roland-Garros sau 14 ciki har da sau hudu a jere. Tarihi ne dai, wanda ba taba samun wani dan wasan Tenis da ya kafa shi ba. Cikin murna Rafael Nadal  wanda ya yi ritaya a bara, ya rasa kalmar da zai yi amfani da ita domin nuna godiyar da zai yi a game da wannan girmamawa. An saka sawun kafar dan wasan mai shekaru 38 a harabar filin wasa na Philippe-Chatrier da ke Paris a matsayin shaida ta tarihin da ya kafa a gasar Tenis ta Rolland-Garros, shaidar da za ta kasance a gurin har a bada.

Kungiyar kwallon kafa ta Stuttgart, zakaran kofin kalubale na JamusHoto: Federico Gambarini/dpa/picture alliance

Kugiyar kwallon kafa ta Stuttgart ta lashe kofin kalubale na Jamus, bayan ta lallasa Arminia Bielefeld da ci 4-2 a karawar karshe da suka yi a ranar Asabar. Wannan nasara ta bai wa Sttutgart damar lashe kofinta na farko tun bayan shekara ta 2007 tare kuma da samun gurbin buga gasar Europa, lamarin da ke nuna yadda ruhin tawagar karkashin Sebastian Hoeness ya farfado a bana duk da ta karkare gasar Bundesliga a matsayi na tara da maki 50 cif. Har wa yau a Jamus din kungiyar Heidenheim za ta kara da Elvesberg a wasan neman makalewa a Bundesliga rukuni na farko bayan gaza tabuka abin a zo a gani a kakar wasa ta bana, inda ta kammala a matsayin na 16 da maki 29 kacal. A zagayen farko dai na wasan da kungiyoyin suka buga a an tashi 2-2 a gidan Heidenheim, lamarin da ke nuna cewa sai ta yi da gaske muddin tana son kaucewa yin abun fallasa.
A Premier League ta kasar Ingila kungiyoyin Manchester City da Chelsea da Newcastle sun yi nasar samun tikitin buga gasar zakarun nahiyar Turai ta badi, bayan kammala kakar bana. Sai dai a wasannin mako na 38 kuma na karshe da aka buga, karawar da Manchester United ta doke Aston Villa din da ci 2-0. Sai dai wannan wasa ya bar baya da kura, inda Aston Villa ta dauki matakin shigar da kara a gaban hukumar da ke kula da gasar ta League Premier kan korafin cewa alkalin wasa ya yi mata ba daidai ba. A Laligar kasar Spain Kungiyar Real Madrid ta gudanar da bikin gabatar da Xabi Alonzo a matsayin sabon mai horas da 'yanw wasanta, wanda zai maye gurbin Carrlo Ancelotti shekaru uku masu zuwa. Alonso mai shekaru 43 a duniya zai yi kokarin fitar wa 'yan farin gida kitse daga wuta, bayan sun yi farar shekara yayin da babbar kishiya Barcelona ta lashe kofuna uku sannan kuma ta casa Madrid din sau hudu a jere.

Manchester City ta sha da kyar wajen samun gurbi a gasar zakarun nahiyar TuraiHoto: Stu Forster/Getty Images
Kwallon na neman juya wa 'yan wasan Mamelodi Sundowns na Afirka ta Kudu bayaHoto: Sydney Mahlangu/BackpagePix/empics/picture alliance

Kungiyar kwallon kafa FC Pyramids ta Masar ta taka wa takwararta Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu birki kan yunkurinta na lashe kofin zakarun nahiyar Afirka CAF, bayan sun tashi canjaras 1-1 a zangayen farko na wasan karshe da suka buga a ranar Asabar a birnin Pretoria. Wannan lamari na tabbatar da jan aiki da ke gaban Mamelodi Sundowns, domin FC Pyramids da ke zama gagara badau a gidanta ta samu matsayi mai kyau na lashe wannan gasa a karon farko a tarihinta. Kungiyar ta Mamelodi Sundowns ita ce ta fara cin kwallo a mintuna na 54, kafin a farke wannan kwallo ana dab da tashi daga wasan. Kungiyoyin biyu za su fafata a ranar daya ga watan Yuni mai zuwa a kasar Masar, wasan zai tabbatar da zakaran nahiyar Afirka na CAF na bana. A wani labarin kuma, kungiyar RS Berkane ta Moroko ta lashe kofin Confederation na Afirka, bayan ta tashi kunnen doki 1-1 da kungiyar Simba Sports ta Tanzaniya amma kuma a jimlar wasannin gida da waje ci 3-1. Wannan dai shi ne karo na uku a cikin shekaru shida da RS Berkane ta Moroko ke lashe wannan kofi, lamarin da ke tabbatar da cewa har yauzu kungiyar na kan ganiyarta.

'Yan wasan RS Berkane sun sake zama zakaraHoto: Nabil Ramdani/BackpagePix/empics/picture alliance

An kammala gasar tsren kekuna ta duniya mai lakabi da Tour Cycliste International du Togo karo na 30 a birnin Lome na kasar Togo, inda Mali ta bai wa marada kunya tare da yin awon gaba da babban tukwici. Dan tsren Mali Diarra Sidiki shi ne ya yi nasarar samun riga mai launin rawaya, bayan fafatawa sau tara a rukunin tseren na kilomita 1,300. A sauran tseren tazara da aka karkare gasar da su, tauraron dan tseren Burkina Faso Ilboudo Soumaila ya haska, inda ya zo na farko yayin da Julien Amadori na Faransa ya zo na biyu sannan Diallo Djandouba na kasar Mali ya zo a matsayi na uku.