Wasanni: Australia ta yi faduwar bakar tasa
February 9, 2026
Australia ta yi faduwar bakar tasa, a zagayen farko na wasanni neman gurbi a gasar Tennis ta Davis Cup. Wannan dai ita ce rashin nasara mafi muni da 'yan wasan Australia suka yi a tsawon shekaru, inda suka sha kashi a hannun Ecuador a Lahadin karshen mako. Australia da ta lashe gasar har sau 28, ta sha kashi ne a lokacin da Gonzalo Escobar da Diego Hidalgo suka lallasa 'yan wasanta Rinky Hijikata da Jordan Thompson da ci bakwai da biyar da shida da hudu.
Ecuador ba ta da 'yan wasa a cikin shahararrun 'yan kwallon tenni 200 na duniya, sai dai wannan nasara ta ba ta gagarumar dama a wasanta na farko na neman tikitin gasar ta Davis Cup. Cikin watan Satumbar wannan shekara ta 2026, Ecuador za ta fafata da Birtaniya a zagaye na biyu.
Daga Amurka kuwa kungiyar Seahawks ta garin Seattle babban birnin Jihar Washington, ta yi nasarar lashe gasar bana ta cin kofin kwallon zari ruga na Amurka wato American Football, bayan da ta doke kungiyar New England Patriot da maki 29 da 13 a wasan karshe da suka fafata a jihar California.
A gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya na lokacin sanyin hunturu da ke gudana a Milan da Cortina na Italiya, zuwa yanzu kasar Norway ke kan gaba da zinare 3, azurfa 1, da tagulla 2 gaba daya tana da lambobi 6. Amurka tana matsayi na biyu da zinare 2, sai Italiya mai masaukin baki da zinare 1, azurfa 2, da tagulla 6 a gaba daya tana da guda 9. A matsayi na hudu akwai Japan mai zinare 1, azurfa 2 da tagulla 1, a gaba daya tana da hudu, yayin da Austria take matsayi na biyar da zinare 1, azurfa 2 a gaba daya tana da uku. Kasar Jamus tana matsayi na shida da zinare 1, da azurfa 1, da tagulla 1 a gaba daya tana uku.
Bayern Munich ta ci gaba da zama daram a kan teburin Bundesliga a bana da maki 54, bayan da ta karbi bakuncin Hoffenheim ta kuma yi mata dukan kawo wuka da ci biyar da daya. Wannan nasara ta dakile fatan abokiyar hamayyarta Borussia Dortmund da ke biye da ita da maki 48 na rage yawan makin da ke tsakaninsu da take ci gaba da kokarin yi. A karshen makon dai, Dortmund din ta bi Wolfsburg har gida ta lallasa ta da ci biyu da daya.
A sauran wasannin na mako na 21 St.Pauli ta karbi bakuncin Stuttgart ta lallasa ta da ci biyu da daya, yayin da Bremen ta sha kashi a gidan Freiburg da ci daya mai ban haushi. An tashi wasa kunnen doki daya da daya tsakanin Union Berlin da Frankfurt, kamar yadda ta kaya tsakanin Borussia Mönchengladbach da Bayer Leverkussen. Hamburg ta bi Heidenheim har gida ta lallasa ta da ci biyu da nema, yayin da Mainz ta karbi bakuncin Augsburg ta caskara ta da ci biyu da nema.
A La Liga ta Spaniya kuwa, Barcelona da ke saman tebur da maki 58 a mako na 23 ta karbi bakuncin RCD Mallorca ta caskara ta da ci uku da nema kamar yadda Athletic Bilbao ta karbi bakuncin Levante ta yi mata dukan kawo wuka da ci hudu da biyu. Real Madrid da ke matsayi na biyu a teburin La Liga da maki 57 kuwa, ta yi tattaki zuwa gidan Valencia ta kuma lallasa ta da ci biyu da nema. Ita kuwa Atlético Madrid da ke matsayi na uku da maki 45, ta karbi bakuncin Real Betis Balompie ta kuma sha kashi a gida da ci daya mai ban haushi.
Yayin da Arsenal ke ci gaba da yin zaman dirshan a saman teburin Premier League ta Ingila da maki 56 kuwa, sannu a hankali Manchester City da ke a matsayi na biyu da maki 50 na shirin cimma ta. A karshen mako Arsenal din ta yi nasara a gida da ci uku da nema a kan takwararta FC Sunderland, yayin da Manchester City ta bi Liverpool har gida ta lallasa ta da ci biyu da daya. Manchester United kuwa da ta dare zuwa mataki na hudu a teburin gasar, ta karbi bakuncin Tottenham ta kuma caskara ta da ci biyu da nema. Aston Villa da ke a matsayi na uku da maki 47 kuwa ta yi tattaki zuwa gidan Bournemouth, inda suka tashi wasa kunne doki daya da daya.
Wasu magoya bayan tawagar kwallon kafar Senegal da ake ci gaba da tsare su a Rabat sakamakon abubuwan da suka faru a lokacin wasan karshe na Gasar cin Kofin Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka, sun fara yajin cin abinci. Matasan su 18 sun shiga yajin cin abinci ne a matsayin nuna adawa da yanayin da suke ciki da kuma rashin cikakken bayani game da tuhumar da ake musu.
A yayin da aka bude fagen fafatawa a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Kwallon Kafa ta Mata 'Yan Kasa da Shekaru 20 ta Duniya kuwa, ana iya cewa Najeriya ta fara da kafar dama bayan da ta lallasa 'yan mtan Senegal da ci daya mai ban haushi a wasansu na farko zagayen farko a filin wasa na MKO Abiola da ke Abeokuta a Najeriya.
'Yan matan Falconets na Najeriyar dai, za su yi tattaki a ranar Asabar din da ke tafe 14 ga wannan wata na Fabarairu zuwa Senegal, inda za su fafata a wasa na biyu a zagayen farko da 'yan matan Lionesses din a birnin Thiès. A watan Satumbar bana ne dai, za a fafata a wannan gasa a kasar Poland, inda a yanzu haka 'yan matan Koriya ta Kudu ke rike da kambunta.