1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni na karshen mako

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
May 5, 2025

Kungiyar Bayern Munich ta sake carar zakara a karo na 34 a tarihin babban lig din kwallon kafar Jamus na Bundesliga, bayan da ta dada lashe gasar a bana.

Labarin Wasanni | Bundesliga | Bayern Munich | Zakara
Bayern Munich zakarar Bundesliga karo na 34Hoto: Gintare Karpaviciute/REUTERS

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta yi abin da masu iya magana kan danganta da mai rabon ganin badi ko ana muzuru ana shaho sai ya gani, sakamakon lashe kambun zakara na Bundesligar Jamus karo na 34 a tarihinta da ta yi duk da canjaras uku da uku da ta yi da RB Leipzig a mako na 32. Wannan nasarar ta samu ne saboda Bayer Leverkusen ta kasa tabuka abin kirki a karawar da ta yi da Freiburg, inda su ma suka tashi canjaras biyu da biyu. Rashin nasarar Leverkussen din da ke matsayi na biyu dai, ta haifar da tazarar maki takwas a tsakaninta da Bayern da ke saman teburin na Bundesliga ta bana.

Kofi na farko ga Harry KaneHoto: Harry Langer/DeFodi Images/picture alliance

Sai dai wannan kambun ya kasance farau ga mutane biyu a tawagar ta Munich: na farko shi ne Harry Kane dan Ingila mai shekaru 31 da ya yi rashin nasara a wasannin karshe guda shida, ciki har da biyu da babbar kungiyar Ingila da kuma wasan karshe da Tottenham a gasar zakarun Turai. Haka ma ita ce ta farko ga Vincent Kompany dan kasar Beljiyam mai asali da kasar Kwango, a matsayin mai horas da 'yan wasa da ya horas da kungiyoyin Anderlech da Burnley da ya yi bayani kamar haka: "Muna son wasanmu na karshe a gida a mako mai zuwa ya kasance mai ban sha'awa. Zai kasance wasan karshe na Thomas Müller a Allianz Arena, kuma Harry Kane zai iya yin bikin samun kambunsa na farko. Akwai dalilai da yawa da za su sa mu yi shiri sosai don tinkarar wannan wasa na gaba. Babu shakka, kafin wannan lokci, za mu yi ci gaba da murna, amma duk da haka za mu shirya tinkarar wasa na gaba."

Vincent Kompany mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bayern MunichHoto: Alex Grimm/Getty Images

A sauran wasannin Bundesliga kuwa, wasu manyan kungiyoyi irin su Borussia Dortmund na ci gaba da fadi tashi don ganin cewar sun samu gurbi a gasannin Turai musamman ma gasar zakaru. Frankfurt ga misali da ta yi kunnen doki daya da daya da makwabciyarta Mainz, ta kusa samun tabbacin samun matsayi na uku da zai ba ta damar shiga gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa. Sannan matsayi na hudu da shi ma ke bayar da tikitin gasar zakarun Turai na hannun Freiburg, amma Borussia Dortmund da ke a matsayi na biyar a teburin Bundesliga ba ta cire tsammani ba bayan da ta yi wa Wolfsburg dan karen duka da ci hudu da nema. Ita kuwa RB Leipzig da ke a matsayi na shida na tsammanin wa rabbuka, duk da rashin tabuka abin kirki a wasanninta na 'yan makonnin da suka gabata. Sai dai kuma ta faru ta kare wa Bochum da za ta koma karamin lig, sakamakon zarrar maki biyar da Heidenheim ta yi mata.

Har ynazu da sauran rina a kaba ga kungiyar kwallon kafa ta Borussia DortmundHoto: Christian Schulze/Nordphoto/IMAGO

A Italiya Napoli ko Naples tana kusa da lashe kambun zakara na Serie A, bayan da ta lallasa Lecce da ci daya mai ban haushi. Wanna dai ya ba ta damar samun maki uku, a gaban Inter Milan da ke a matsayi na biyu. A Spaniya kuwa FC Barcelona na ci gaba da jin kamshin kambun La Liga, duk da cewa abokiyar gaba Real Madrid ta kasa mika kai domin bori ya hau. Ita dai Barcelona da ta doke Valladolid da ci biyu da daya tana kan gaba da maki hudu, inda Madrid da ta samu nasara a kan Celta Vigo da ci uku da biyu. A yayin da ya rage wasanni hudu a kawo karshen kakar gasar ta La Liga, 'yan wasan da Hansi Flick ke horaswa na fatan samun makomarsu a hannun bayan sun kara da Real Madrid a ranar Lahadin, kwanaki kalilan bayan wasansu na kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.

FC Barcelona na da sauran aiki kafin ta lashe La Liga ta banaHoto: Jose Breton/AP/picture alliance

Har yanzu dai muna fannin kwallon kafa amma a wannan karon a Afirka, inda ake gudanar da gasar 'yan kasa da shekaru 20 na wannan nahiya a kasar Masar. A wasannin rana ta biyu a rukunin farko da suka gudana a jiya, Saliyo da ke zama 'yar auta ta samu nasara ta biyu a jere  ta hanyar lallasa Tanzaniya da ci daya mai ban haushi kuma tana gab da zuwa wasan kusa da na karshe na farko a tarihinta. A nata bangaren, Tanzaniya ta kama hanyar komawa gida, saboda gaza nasara a wasanninta biyu da ta yi. Ita kuwa Masar mai masaukin baki tana da maki hudu a wasanni biyu, bayan da ta yi canjaras babu ci a wasanta da Zambiya. A rukuni na B kuwa Tunisiya ta doke Kenya da ci uku da daya, yayin da Maroko da Najeriya suka tashi canjaras babu ci. A halin yanzu ma dai, kungiyoyin biyu ne suka mamaye wannan rukunin da maki hudu kowaccen su. A wasannin rukuni na uku da ya hada Senegal mai rike da kofin da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Ghana kuwa, na gudana a wannan Litinin din.

Tawagar Ghana na cikin rukuni na ukuHoto: Metin Pala/AA/picture alliance

Tsibirin Seychelles na ci gaba da daukar bakunci gasar duniya ta kwallon kafar bakin teku da ke gudana a kan yashi, inda ake da wakilai biyu daga nahiyar Afirka wato Muritaniya da Senegal da ke rike da kofin Afirka a halin yanzu. Hasali ma dai, 'yan Senegal sun tabbatar da fatan da ake musu ta hanyar samun nasara da ci shida da uku a wasansu da Tahiti. Wannan ita ce nasara ta biyu a wsanni biyu da 'yan Senegal suka samu bayan da a ranar Jumma'a suka lallasa Spaniya da ci hudu da daya, lamarin da ya sanya Senegal ita kadai a saman teburin rukunin C da maki shida a wasanni biyu. A wannan litinin ake ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafar bakin tekun ta duniya, inda a rukunin B Muritaniya da ke ci gaba da neman nasarar farko, za ta fafata da Paraguay a wasan da ke zama damar karshe ga 'yan wasan Muritaniyan ko kuma su tattara nasu ya nasu su koma gida.

Gasar teren keke na kara samun karbuwa a AfirkaHoto: Gian Ehrenzeller/KEYSTONE/picture alliance

Yanzu kuma sai tseren keke na kasa da kasa da aka kammala a birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin, inda wani dan kasar Philippines mai suna Marriage Zakary ya lashe matakin karshe yayin da dan kasar Afirka ta Kudu Reinardt Janse Van Rensburg ya samu damar lashe gasar ta bana. Kazalika, dan tseren Afirka ta Kudun ya lashe gasar Grand Prix na Cotonou da hukumar tseren keke ta duniya UCI ke daukar nauyi kuma ke gudana bayan tseren keken kewaye Benin. Haka su ma mata ba a bar su a baya ba, inda a karon farko suka gudanar da tseren keke da ake wa lakabi da Grand Prix International des Amazones a birnin Coronou. Awa Bamogo daga Burkina Faso ce dai, ta kasance zakaran wannan gasa.