1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damben boxing da wasan guje-guje da kwallon kafa

Abdourahamane Hassane MNA
February 17, 2020

Caleb Plant ya kare kambunsa a damben boxing, sannan Cater Semenya za ta koma filin wasa, yayin da Zamalek ta laseh gasar Super Cup.

Caleb Plant bayan ya doke Vincent Feigenbutz
Caleb Plant bayan ya doke Vincent FeigenbutzHoto: picture-alliance/AP Images/M. Humphrey

Caleb Plant dan Amirkan nan ya yi nasara rike kambusa na zakaran duniya a damben boxing na masu matsakaicin nauyi. Ita ma Caster Semenya 'yar wasan gudun tsere ta Afrika ta Kudu zakara a wasan Olympik a shekara ta 2012 da 2016 ta koma fagen daga bayan da ta tsaiyar da wasan tsawon lokaci. Kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta Zamalek ta lashe gasar Supercup a Doha a kasar Qatar amma kuma manazarta na yin muhawara a game da gasar za kuma mu leka a filayen kwallon kafa  na Jamus don jin irin wainar da aka toya a karshen mako.

Shi dai dan damben boxing kuma dan kasar Amirka, Caleb Plant ya yi nasarar kare kambusa na zama zakara a ajin masu matsakaicin nauyi na IBF, inda ya doke Vincent Feigenbutz dan kasar Jamus a zagaye na goma a karawar da suka yi a Nasville a Amirka.

Caster Semenya a wani tseren mita 800 na Daimond League a Doha, QatarHoto: Getty Images/F. Nel

Caster Semenya 'yar wasan motsa jiki ta yi nasara a gasar tsere ta mita 300 a birnin Johanesburg na kasar Afirka ta Kudu bayan da ta kwashe watanni bakwai da tsaida wasan a karkashin wata doka ta kasa da kasa da ta hana ta yin kwambala saboda halitta ta yawan wani sinadarin da take da shi "Testosterone" na mace kamar maza. Semenya wacce ta samu lambar zinari a wasan Olympik na shekara ta 2012 da 2016 ta yi nasarar zuwa ta farko a cikin dakiko 36 a gasar.

A karshen mako a mako na 22 na wasannin Bundesliga a ranar Jumma'a kungiyar Dortmud ta doke Frankfurt da ci hudu da nema, sannan a ranar Asabar Fortuna Düsseldof ta fadi a gaban Mönchengladbach da ci hudu da daya, Bayer Leverkusen kuma ta yi wa Union Berlin ci uku da biyu, Hertha Berlin ta samu nasara a kan Paderborn da ci biyu da daya, Ausbourg kuma da Freiburg an yi kunnen doki kowanne na da ci daya a yayin da Wolfsburg ta yi wa Hoffenheim ci uku da biyu. Ita kuwa Leipzig rabani da yaro ta yi wa Bremen da ci uku da nema.

Serge Gnabry da Alphonso Davies bayan da Gnabry ya saka kwallo a ragar Cologne Hoto: picture-alliance/Fotostand/Wundrig

A ranar lahadi Bayern Munich ta doke Cologne da ci hudu da daya kana Mainz da Schalke suka tashi ba wanda aka ci. Kungiyar Byern Munich ta kare matsayinta na farko a teburin kwallon kafar Bundesliga da maki 46, Leipzig na biye da maki 45 sai Dormund a matsayi na da maki 42. 

A ranar Jumma'a da yamma aka yi wasan karshe na cin kofin Super Cup a birnin Doha na kasar Qatar, inda kulob din Zamalek na kasar Masar ya samu nasara a kan Esperances na kasar Tunisiya da ci uku da daya.