'Yan Kenya sun kafa tarihi a gudun dogon zango
October 14, 2019A karshen mako a birnin Vienna na kasar Ostriya yayin gudun fanfalaki ko dogon zango da aka gudanar, Eliud Kipchoge dan kasar Kenya mai shekaru 34 da haihuwa ya kafa gagarumin tarihi wajen kammala tseren cikin kasa da sa'o'i biyu kacal, wato sa'a guda da mintoci 59 da dakikoki 40 a wannan gudun na tsawon kilomita 42 da mita 195.
Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya ya kira dan wasan domin taya shi murnar wannan gwaninta da kara fito da sunan kasar a idon duniya.
Haka ita ma Brigid Kosgei 'yar shekaru 16 da haihuwa daga kasar ta Kenya ta kafa wani tarihin yayin gudun fanfalaki na mata a birnin Chicago na kasar Amirka lokacin da ta kammala gudun cikin sa'o'i biyu da mintoci 14 da dakikoki 4.
Wasannin sada zumunci
A karshen makon an kara wasannin sada zumunta tsakanin kasashen duniya, inda Najeriya ta tashi 1 da 1 da kasar Brazil yayin wasa a Singapore, sannan Mozambik ta doke Kenya 1 da nema, ita kuma kasar Afirka ta Kudu ta samu nasara kan Mali 2 da 1, haka ma Yuganda ta doke Habasha 1 mai ban haushi. Equatorial Guinea da Togo sun tashi 1 da 1.
Ita kuwa Ajentina ta yi wa Ecuador cin kacar tsohon keke rakacau 6 da 1. Jamhuriyar Benin da Zambiya sun tashi 2 da 2, Kasar Cote d'Ivoire ta doke Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango 2 da 1, kana Slovakiya da Paraguay 1 da 1.
Sai tsallaka zuwa wasannin zari-ruga na duniya da ke wakana a kasar Japan inda aka soke wasannin da aka tsara a karshen mako sakamakon guguwa mai karfi dauke da ruwan sama suka ratsa kasar tare da haifar da ta'adi mai munin gaske. Duk da haka a wasan da aka kara Japan mai masaukin baki ta tsallake rijiya da baya wajen doke Scotland domin kai wa ga wasan kusa da na kusa da na karshe a wasannin na zari-ruga.