Wasanni karshen mako cikin shirinmu na labaran wasanni
September 22, 2025
A ciki muna dauke da wasannin lig-lig da aka kara a kasashen Turai. Sannan an kammala wasannin motsa jiki na duniya da ya gudana a birnin Tokyo na kasar Japan. Akwai ma wasu fannonin wasannin, kamar karawa da aka yi a wasannin Bundesliga ta Jamus, Inda aka tashi:
-Stuttgart 2, St. Pauli 0
-Bremen 0, Freiburg 3
-Augsburg 1, Mainz 4
-Hamburger SV 2, Heidenheim 1
-RB Leipzig 3, Cologne 1
-Sunday's Matches
-Eintracht 3, Union Berlin 4
-Leverkusen 1, Monchengladbach 1
-Dortmund 1, Wolfsburg 0
Kuma wasan da Hoffenheim 1, Bayern Munich 4 muka gabatar muku kai tsaye, inda aka jefa kwallon na karshe na hudun bayan karin lokacin yayin da kuma ake shirin kawo karshen wannan sharhin wasanni.
Har yanzu dai kungiyar Bayern Munich ke jagorancin teburin na Bundesliga a Jamus da maki 12, yayin da Borussia Dortmund ke matsayi na biyu da maki 10, kana a matsayi na uku akwai Leipzig da maki 9, ita kuwa kungiyar FC Kolon ta masatyi na hudu da maki 7.
A wasannin Firimiya da aka kara a Ingila, kungiyar Manchester United ta doke Chelsea 2 da 1, Sunderland da Aston Villa sun tashi 1 da 1, haka Arsenal da Manchester City sun tashi 1 da 1, FC Fulham ta doke Brentford 3 da 1, yayin da Leeds ta bi Wolverhampton har gida ta doke ta 3 da 1.
A wasannin La Liga da aka kada a kasar Spain, kungiyar Real Madrid ta doke Espanyol 2 da nema, Barcelona ta yi raga-raga da Getafe 3 da nema.
Daya daga cikin fitattun masu tseren motoci na Formula 1, Lewis Hamilton ya ce zai bai wa abokinsa Charles Leclerc da suke kungiyar guda a tawogar motocin Ferrari hakuri, saboda rashin iya mayar masa da matsayinsa lokacin gasar da aka gudanar a wannan Lahadi da ta gabata a kasar Azerbaijan. 'Yan wasan sun kammala a matsayi na tara a gasar ta birnin Baku. An dai samu gibi lokacin da 'yan wasan biyu Lewis Hamilton da Charles Leclerc suka yi sauyi.
A karshen mako aka kammala wasannin motsa jiki na duniya wanda ya gudana a birnin Tokyo na Japan daga ranar 13 ga watan Satumba zuwa 21. ‘Yan wasa sama da dubu biyu ne suka fafata a wasanni 49 don neman lambobi 147 da aka bayar a wasannin. Pinado Waba na dauke da Karin bayan.