Gasar FIFA Club World Cup cikin LAbarin Wasanni
June 16, 2025
A gasar cin kofin zakarun kungiyoyin duniya wato FIFA Club World Cup a Amurka a ranar 15 ga wannan wata na Yuni, inda kungiyoyi 32 daga nahiyoyi dabam-dabam na duniya ke can suna barje gumi a wasannin rukuni. A rukunin C, Bayern Munich ta kasar Jamus ta ragargaza kungiyar Auckland City ta kasar New Zeland da ci 10da nema ciki har da kwallaye uku da matashin dan wasa Jamal Mussiala ya zura da kuma kwallaye biyu na tsoho Thomas Müller. Sai dai duk da wannan abun fallasa da tawagar ta Auckland City ta yi, mataimakin mai horas da 'yan wasan kungiyar ta kasar New Zeland Ivan Vicelich ya ce ya gamsu da rawar da 'yan wasansa suka taka a gaban guda daga cikin manyan kungiyoyi a wannan gasa.
Kungiyoyi hudu ne ke wakiltar nahiyar Afirka a wannan gasa, uku daga yankin kasashen Larabawa da suka hada da Al Ahly ta Masar da Wydad Casablanca ta Mororko da Esperance de Tunis ta Tunisiya sai kuma Mamelodi Sundowns daga Afirka ta Kudu. A wasan farko da aka yaye labulen gasar da shi a rukunin A, kungiyar Al Ahly ta kasar Masar wadda ta lashe kofin zakarun Afirka sau 12 ce ta taka wa Lionel Messi da takwarorinsa na Inter Miami birki a wasan da suka tashi babu ci. A yanzu Bayern Munich ke rike da mastsayi na farko a rukunin C, bayan Palmeiras ta kasar Brazil da Porto ta Portugal sun tashi wasa babu ci.
A rukunin B kuwa ita ma kungiyar PSG ta Faransa da ke rike da kofin zakarun nahiyar Turai ta yi wa Atletico de Madrid ta kasar Spaniya sakiyar da ba ruwa, inda ta doke ta da ci 4 da nema. Godiya ta tabbata ga 'yan wasa Fabian Ruiz da Vitinha da Senny Mayulu da kuma Lee Kang-in wanda suka tisa tawagar ta Luis Enerique a matakin farko a wannan rukuni na B, yayin da Botafogo ta kasar Brazil da ta doke Seatle Sounders ta Amurka da ci biyu da daya ke a matsayi na biyu. Za a dai shafe wata guda ana gudanar da wannan gasa karo na 21 a Amurka, inda za a kammala a ranar 13 ga watan Yuli mai zuwa.
Kungiyar SC Magdeburg ta Jamus ta lashe kofin zakarun nihiyar Turai na kwallo hannu a karo na biyar a cikin tarihinta, bayan ta doke takwararta ta Berlin da ci 32 da 26 a wasan karshe. Kungiyar ta Magdeburg da ta fito daga gabashin Jamus ta sake gwada kwanjinta ne tare da daukar fansa bayan rashin nasara da ta yi a wasan karshe na gasar a kakar bara, inda FC Barcelona ta yi awon gaba da kambun. Wannan nasara dai na nuni karara da bajintar kungiyoyin Jamus a fagen kwallon hannu a duniya, domin a kakar ta bana uku daga cikin kungiyoyi hudu da suka wakilci kasar sun kai matakin karshe na gasar.
A gasar tseren motoci ta Formul 1 George Russell na kamfanin Mercedez ya lashe zagaye na 10 na Grand Prix du Canada, bayan hamayya mai sarkakiya tsakaninsa da McLaren a zagayen da'irar Gilles-Villeneuve a birnin Montreal. Dan tseren dan kasar Birtaniya ya doke takwaransa Max Verstappen dan kasar Holland, wanda ya zama zakaran duniya har sau hudu.