1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Labarin Wasanni: Wa zai dauki kofin AFCON?

Suleiman Babayo LMJ
February 5, 2024

A gasar neman cin kofin kasahen Afirka da ke wakana a kasar Cote d'Ivoire Najeriya ta kai wasan kusa da na karshe, inda za ta kara da Afirka ta Kudu ita kuma mai masaukin baki da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Wasan neman cin kofin Afirka
Wasan neman cin kofin AfirkaHoto: Samuel Shivambu/ BackpagePix/empics/picture alliance

Bayan kammala wasannin kusa da na kusa da na karshe a gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2023 AFCON, Najeriya za ta kara da kasar Afirka ta Kudu yayin da mai masaukin baki ta Cote d'Ivoire za ta kece raini da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a wasannin kusa da na karshe.

 

Wasan BundesligaHoto: Jan Huebner/IMAGO

A wasannin Bundesliga da ke gudana a Jamus kuwa, ga yadda wasannin suka gudana a karshen mako tsakanin kungiyoyin:

Heidenheim          0     Dortmund            0

Bayern                  3     Monchengladbach 1

Freiburg               1     Stuttgart               3

Mainz                   0     Bremen                1

Bochum                1     Augsburg             1

FC Kolon              2     Eintracht              0

Darmstadt            0     Bayer Leverkusen 2

 

Lig na IngilaHoto: Jon Super/AP Photo/picture alliance

A gasar Premier League ta Ingila kuwa, kungiyar Manchester United ta doke West Ham da ci uku da nema, ita kuma Burnley da FC Fulham sun tashi canjaras biyu da biyu, yayin da Arsenal ta doke Liverpool da ci uku da daya.

Faransa ta samu nasarar wauce matakin rukuni a gasar neman cin kofin Davis ta Tennis bayan doke Taiwan. Haka kasashen Sabiya da Netherlands da Finland da Jamus da Brazil da Amurka da Kanada suna cikin wadanda suka tsallaka.

Tsohon shahararren dan wasan Zari-Ruga na Wales Barry John tsohon shahararren dan wasan Zari-Ruga na Wales, ya rigamu gidan gaskiya. Marigayin da ake kiransa da sunan sarki lokacin da yake ganiyarsa a wasan na Zari-Ruga, ya bar duniya yana da shekaru 79 bayan ya sha fama da rashin lafiya.