1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayern ta ci gaba da zama a saman tebur

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
February 21, 2022

Wasannin olympics na lokacin sanyi sun kammala a birnin Beijing, inda Noway da Jamus da Chaina suka fi samun lambobi. Muna tafe da sakamakon wasannin Bundesliga na Jamus.

Chaina | Olympics 2022 | Beijing I Italiya
Kasar Italiya ce za ta karbi bakuncin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympics a 2026Hoto: Paul Hanna/UPI Photo/imago images

Bayan da aka shafe makonni biyu na gasar ta Olympcis ta lokacin hunturu, an samu ci gaba a wasanni da yawa yayin da rigingimu da dama suka bayyana a gasar. Gwamnatin kasar Chaina ba ta fuskanci wata badakala ko suka da daga bangaren 'yan wasa ba, duk da kaurace mata a diflomasiyance da kasashen Yamma da dama suka yi kan zargin da suke mata na tauyin hakkin dan Adam da tsirarun Musulumin kasar. Dama dai shugaban kasar Xi Jinping ya bayyana cewa, ba yawan lambobin da tawagar kasarsa ta samu ne mai muhimanci ba walwalar 'yan wasa ne ke da muhimmancin gaske. 'Yar wasan tseren kankara da ke wakiltar kwamitin Olympics na Norway ne suka zo na daya a gasar da lambobi 37 ciki har da zinare 16, yayin da takwarorinsu na Jamus ke biye musu baya da lambobi 27 ciki har da zinare 12. Ita kuwa Chaina mai masaukin baki ta samu lambobi 15 ciki har da zinare 09. Amma 'yan wasan da suka wakilci kasashen Afirka ba su samu ko da lamba daya ba, wanda dama an san za a rina saboda wasan kankara ba shi da tasiri a wannan nahiya.

Kungiyar ta Bayern Munich, ta ci gaba da zama daram a saman terburin Bundesliga Hoto: Alexander Hassenstein/Getty Images

A wasannin mako na 23 na Bundesligar Jamus, mako guda bayan doke ta da Bochum ta yi Bayern Munich ta yi wasa cikin natsuwa da karsashi da kurar baya Greuther Fürth. Bayern Munich ta fara ne da sakaci a mintunan farko na karawa da Greuther Fürth, inda aka fara zira mata kwallo kafin a tafi hutun rabin lokaci. Daga bisani ne ta farfado daga magagin da ta fada, inda bayan farke kwallon da ake binta ta zazzaga karin kwallaye uku. Wannan nasarar hudu da dayan, ta zo ne mako guda bayan mawuyacin halin da ta fada ta dibi kashinta a hannun 'yan baya ga dangi Bochum a gasar Bundesliga yayin da ta yi kunnen doki da Salzburg a gasar zakarun Turai. Bayern Munich na ci gaba da yi wa Borussia Dortmund ratar maki shida, wacce ita kuma ta yi wa takwararta Borussia Mönchengladbach dukan kawo wuka da ci shida da nema. Ita kuwa Bayer Leverkusen ta doke Mainz da ci uku da biyu, lamarin da ya sanya ta a matsayi na uku a teburin Bundesliga. Sai dai kuma fafatawar neman gurbi na hudu kuma na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, na ci gaba da zafafa tsakanin kungiyoyi uku. Kungiyoyin RB Leipzig da Hoffenheim da kuma Freiburg na da maki 37 kowacensu, bayan da suka yi nasara a karshen wannan mako a kan Hertha Berlin da Wolfsburg da kuma Augsburg.

Fitaccen dan wasan kwallon Tennis na duniya, Novak DjokovicHoto: John Walton/PA Wire/empics/picture alliance

Makonni da dama bayan korarsa daga gasar Ostiraliya sakamakon rashin riga-kafin COVID-19, Novak Djokovic zai shiga a dama da shi a gasar Dubai. Ba a bukatar allurar riga-kafin corona wajen shiga gasar Dubai da ke Hadadiddiyar Daular Larabawa, saboda haka ne dan asalin Sabiyan Novak Djokovic wanda har yanzu shi ne na daya a duniya a fagen tennis, zai yi kokarin kare matsayinsa duk da lokacin da ya dauka ba tare da ya yi wasa ba. Burin da Djokovic ya sa a gaba dai shi ne ci gaba da rike kambun gwani na gwanaye Tennis na duniya, wanda dan wasa mai matsayi na biyu a ATP Daniil Medvedev dan kasar Rasha da hari a  gasar Acapulco da yake halarta. Idan ko Medvedev wanda ya yi wasan karshe na gasar Australian Open ya lashe gasar Mexico, babu makawa zai zama sabon dodon tennis na duniya ko da "Djoko" ya zo na daya a Dubai. Tun ranar 3 ga watan Disambar bara ne Novak Djokovic bai yi shiga muhimmiyar gasa ba, bayan rashin nasara a Madrid da kasarsa Serbia ta yi a karawa da Croatia a wasan kusa da na karshe na cin kofin Davis.