1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Soke gasar Firimiyya a Najeriya saboda Covid-19

Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
July 13, 2020

Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya NFF ta ba da sanarwar soke gasar kwallon kafa ta kakar 2019/2020 saboda annobar Covid-19 da ta addabi duniya.

Nigeria Lagos Fußball-Fans mit Smartphones
Hoto: Getty Images/AFPP.U. Ekpei

A karshen mako Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, NFF, ta ba da sanarwar soke gasar kwallon kafa taFirimiyyata kakar 2019/2020 saboda Covid-19. Yanzu dai an dakatar da gasar a mako na 25 wanda hakan ke nufin ba za a karasa ba. Amma kuma kungiyoyin da suke mataki na daya zuwa na uku sun samu tikitin zuwa gasar zakarun nahiyar Afirka, bayan da NFF din ta yi amfani da tsarin ba da maki na "Points Per Game" ta yanke matsayin kowace kungiya a teburin Firimiyyar.

Shahararren dan wasan damben nan dan Najeriya da ke da jini da Amirka, Kamaruddeen Usman, ya sake lashe kambun gasar dambe ta UFC.

Shi dai dan damben ya yi kokarin ci gaba da rike kambunsa na zakaran wasan damben ajin masu matsakaicin nauyi na UFC bayan da ya samu nasara a kan abokin karawarsa Jorge Masvidal. An dai kammala wasan babu kisa, inda daga bisani Kamaru da ake wa lakabi da dodon dambe dan Najeriya, ya lashe wasan bisa hukuncin alkalan wasa. Alkalan wasa biyu dai sun bayyana cewa Usman ya lashe wasan da maki 50 yayin da abokin karawasa ke da 45, yayin da alkali guda ya ce ya samu maki 49 shi kuma Masvidal na da 46.

Hoto: picture-alliance/Geisler-Fotopress

Za kuma mu koma kan batun kwallon kafa, inda a kakar wasannin la liga ta kasar Spain, a yanzu haka kungiyar Real Madrid da ke kan gaba da maki 80 a teburin kakar ta bana na fuskangtar gagarumin kalubale, da ke nuni da cewa tilas ta klashe wasan da za ta yi da yammacin yau tsakaninta da Granada, idan kuwa ba haka ba za ta kasasnce cikin tsaka mai wuya, domin kuwa ana ssauran wasanni biyu a kakar ta bana, maki guda ne kacal a yanzu haka tsakaninta da mai biye mata wato kungiyar Bercelona, in kuwa ta samu nassara zai kasance tazarar maki hudu ne a tasaknaisu, wandda hakaan ka iya ba ta fata na lashe kakar ta bana. A wani labarin kuma, jagoran kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Josep Maria Bartomeu ya nunar da cewa sun dakatar da tattaunawar da suke yi da kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan kan cinikin dan wasan gaba na Inter Milan din Lautaro Martinez dan asalin kasar Argentina, mai shekaru 22 Martinezya zura kwallaye 17 kungiyarsa ta Inter Milan a kakar wasanni ta bana.

Idan muka koma kan gasar Bundesligar kasar Jamus kuwwa, an fito da jadawalin wasnni na kakar wasannin ta badi, inda ake sa ran buga wasan farko a rahankun 18 zuwa 21 ga watan Satumbar bana, yayin da za a tafi hutun lokacin hunturu a ranar 22 ga watan Disamba a kuma dawo filin daga ranar daya ga watan Janairun 2021. Ana dai sa ran kammala kakar wasannin a ranar 22 ga watan Mayu na shekara mai zuwa ta ta 2021.

Mai tuka motar kamfanin Mercedes, Lewis Hamilton a tseren motoci na Formula 1Hoto: Reuters/J. Klamar

Bari mu kakrkare da wasan tseren motoci na Formula 1, inda fitaccen dan wasan tseren motocin da ke tuka motar kamfanin motoci na Mercedes, Lewis Hamilton ya samu nasarar lashe gasar tseren motocin zagaye na biyu a kasar Ostiriya. Dama dai dan tseren motocin na duniya dan kasar Birtaniya, ya lashe zagayen farko da aka gudanar a makon da ya gabata, abin da ke nuni da kare kambunsa na zakaran tseren motoci na duniya.