1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasannin karshen mako, cikin Labarin Wasanni

September 15, 2025

An yi ruwan kwallaye a mako na uku na kakar Bundesligar Jamus ciki har da tonon silili a Bremen ta yi wa Mönchengladbach a gaban magoyabayanta.

Jamus | Bundesliga | Leverkusen 2025 | Kasper Hjulmand
Sabon mai horas da 'yan wasan Bayer Leverkusen Kasper Hjulmand Hoto: Martin Meissner/AP Photo/picture alliance

Za mu yaye labulen shirin da gasar Bundesliga ta Jamus, inda aka yi gurmuzu a filaye dabam-dabam a wasannin mako na uku. A ranar Jumma'a Leverkusen ta sake farfado da ruhinta, a karkashin sabon mai horaswa Kasper Hjulmand ta doke Frankfurt ci uku da daya. A ranar Asabar Borussia Dortmund ta yi abin kai, inda ta iske Heidenheim har gida ta doketa ci biyu da nema.

Wasan da aka yi tata-burza a cikinsa kuwa shi ne, FC Collogne da ta kai ziyara gidan Wolfsburg  gidanta, a wani wasa mai cike da rudani da kungiyoyi suka buga a cikin yanayi na saukar ruwan sama mai karfi. An dai tsayar da karawar har sau uku, saboda ruwan sama da kuma yamutsi daga 'yan kallo. Amma duk haka a cikin karin muntuna 14 da alkalin wasa ya yi, FC Collogne ta yi nasarar farke kwallo na uku da aka zura mata, lamarin da ya sa kungiyoyin suka tashi canjaras uku da uku.

Gumurzun VfL Wolfsburg da FC CologneHoto: Ralf Treese/DeFodi Images/picture alliance

A sauran wasanni kuwa Union Berlin ta yi abin fallasa a gida, inda ta yi rashin nasara a gaban Hoffenheim da ci biyu da hudu. Mainz kuwa, ta sha kashi a wasanta da RB Leipzig da ci daya mai ban haushi. Freiburg ta doke Stuttgart da ci uku da daya, yayin da Bayern Munich ta yi nasara a kan Hamburg ta hanyar zazzaga mata kwallaye biyar da nema. Wannan wasa ya kasance mai cike da tarihi ga sabon dan wasa Nicolas Jackson dan kasar Senegal da Bayern Munich ta cefano daga Chelsea, domin shi ne karo na farko da ya taka wa sabuwar kungiyarsa leda.

Real Madrid ta sha da kyar a mako na hudu na gasar La Liga ta SpaniyaHoto: Adam Hunger/AP/picture alliance

A sauran Lig-lig na Turai a daf da fara gasar Zakarun Turai, kungiyoyin da ke ji da kansu sun gwada kwanji a filaye dabam-dabam. A La Liga ta Spaniya da kyar da jibin goshi, Real Madrid da ke rike da teburin gasar ta doke Real Sociedad ci biyu da daya. Atletico Madrid da ke a matsayi na 10 ta lallasa Villarreal da ci biyu da nema. Ita kuwa Barcelona kwallaye shida ta zazzaga a ragar Valancia, a wassan da dan tatsitsin yaro da idon duniya ke kansa Lamine Yamal bai buga ba. Sai dai Lewandoski da Rafinha da Firmin Lopez da kowannensu ya ci kwallo biyu, su ne suka jagoranci wannan nasara a mako na hudu na kakar Liligar ta bana.

Bukayo Saka na cikin 'yan wasan da kungiyar Arsenal ke ji da suHoto: Neal Simpson/Imago Images


A Premier League ta Ingila kuwa, manyan wasanni da aka buga a mako na hudu na kakar bana sun hada da dukan kawo wuka da Arsenal ta yi wa Nottingham Forest da ci uku da nema.  Everton ta tashi canjaras da Aston Villa, ba tare da kowannensu ya ci kwallo ba. Tottenham ta iske West Ham har gida, ta casa ta da ci uku danema. Brentford ta yi wa Chelsea ba-zata, inda suka tashi canjaras biyu da biyu. Liverpool da ke saman teburin gasar, ta doke Burnley ci daya mai ban haushi. Sai kuma Manchester City da ta nunawa takwararta Manchester United iyakarta, inda ta lallasata da ci uku da nema ciki har da kwallaye biyu da Haaland ya zura.

Ko wacce kungiya ce za ta lashe gasar Champions League a bana?Hoto: Waldemar Thaut/Zoonar/IMAGO

Talata 16 ga watan Satumbar da muke ciki ne za a yaye labulen gasar Zakarun Turai wato Champions League a cikin sabon fasali, inda za a yi gumurzu a tsakanin kungiyoyi 28 da suka samu tikitin zuwa gasar. Daga cikin manyan wasannin da za a fafata, a yayin bude gasar Altetico Bilbao ta Spaniya za ta karbi bakuncin Arsenal. Real Madrid za ta fafata da Olympique de Marseille ta Faransa, Juventus kuma ta karbi bakuncin Borussia Dortmund. Benfica ta Portugal za ta kara da Qarabag ta Azerbaidjan, sai Tottenham da za ta kece raini da Villarreal ta Spaniya.

A Laraba 17 ga watan na Satumbar 2025, Bayern Munich za ta karbi bakuncin Chelsea. Liverpool kuwa za ta kece raini da Altelico da Madrid, Ajax Amsterdam za ta karbi bakuncin Inter Milan kana Olympiacos za ta kara da Pafos. A ranar Alhamis 18 ga watan na Satumbar 2025 kuwa, Kobenhavn za ta karbi bakuncin Bayer Levekusen, sai kuma Barcelona za ta yi tattaki zuwa Newcastle.

Kungiyar Mannschaft ta Jamus da ta lashe gasar kwallon kwando ta na hiyar TuraiHoto: sampics/picture alliance

Tawagar Mannschaft ta Jamus ta lashe kofin nahiyar Turai na kwallon kwando a karo na biyu bayan 1993, inda ta doke Turkiyya da ci 88 da 83 a wasan karshe da suka fafata a kasar Lithuania. Wannan nasara da Mannschaft ta samu a gaban dumbin 'yan kallo ciki har da shugaban kasar Frank-Walter Steinmeier na zuwa ne, shekaru biyu bayan da tawagar ta lashe kofin duniya na kwallo kwando. Godiya ta tabbata ga kyaftin din Jamus Dennis Schröder wanda shi ne ya yi awon gaba da kyautar dan wasan da ya fi nuna bajimta a wannan gasa, hasali ma Bajamushen mai shekaru 32 a duniya shi ne ya zura kwallaye shida na karshe da suka bai wa Jamus din nasara a wannan karawa mai cike da kalubale.