Wasannin Olympic na lokacin kankara
November 22, 2017Talla
Kafofin yada labaran kasar Rasha sun yi kashedin cewar ba zasu nuna wasannin a gidajen talabijin dinsu ba, matsawar dai aka haramta wa 'yan wasan kasar ta Rasha halarta a bisa dalilin binciken amfani da kwayoyin kara kuzari.
A farkon watan Disamba mai zuwa ne dai hukumar kula a wasannin na Olympic za ta bayyana matsayinta a kan batun badakalar shan kwayoyin masu kara kuzari da aka zargin 'yan wasan kasar Rashar sun yi amfani da su