1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaFaransa

Wasannin Olympics na fuskantar barazana ta hare-hare

Abdourahamane Hassane
July 26, 2024

Ruwan sama a birnin Paris da kuma zagon kasa na layin dogo na Faransa, na yin barzana ga dagula harkokin wasannin Olympics sa'o'i kadan gabanin bude gasar da za a soma a yau zuwa da yamma.

Hoto: Denis Charlet/AFP

 Kamafanin sufirin jiragen kasa na Faransa , SNCF ya sanar da cewar wasu,sun kai hare-hare a kan hanyar layukan dogon abin da ka iya gurgunta sha'anin zirga-zirga na fasinjoji fiye da dubu 800.Kamfanin ya ambato cewar a wurare da dama an tayar da gobara ta da gangan, wacce ta lalata kayayyakin aikinsu. Yanzu haka jami'an leken asirin Faransa  na ta yin bincike domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika, a cewar wata  majiyar ta tsaro.