Wasannin Olympics da hakkin dan Adam
February 7, 2014An bude gasar Olympics ta lokacin hunturu karo na 22 a yankin shakatawa na Sochi da ke kudancin kasar Rasha. 'Yan wasa kimanin 2900 daga kasashe 87 za su fafata don neman cin lambobin zinari, tagulla da kuma azurfa. Sai dai tun kafin bikin bude wasannin, gwamnatin Rasha da kuma kwamitin shirya wasannin Olympics na kasa da kasa sun sha suka da kakkausan lafazi game da take hakkin dan Adam.
Tun da farko dai magana ake game da gasar da za ta fi kowace kayatarwa. An kashe kudi dalar Amirka miliyan dubu 37.5 wajen gina filayen wasa, gidajen da 'yan wasa za su zauna, manyan hanyoyi da kuma otel-otel. A takaice dai wasannin Olympics din na lokacin hunturun a yankin na Sochi shi ne mafi tsada a wannan zamani, musamman ta bangaren take hakkin dan Adam.
Rusau, cin zarafi da kame jama'a
Baya ga rushe-rushen gidajen jama'a, an ci da gumin ma'aikata, an ajiyesu a wurare marasa kyau, kana sun yi aikin gina filayen wasan ba tare da wani kwantaragi ko albashin da ya dace da aikin da suka yi ba, inji Wolfgang Büttner na kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch.
"An yi ta kamewa tare kuma da tursasa wa masu sukar yadda aka gudanar da aikin ginin da yadda aka ci zarafin dan adam. Tun a shekarar 2009 aka san irin matsalolin keta hakkin dan Adam dake tattare da aikin gina wuraren wasannin Olympics na Sochi. Amma sai da aka kusa bude gasar kwamitin Olympics IOC ya dauki matakin matsa kaimi kan hukumomin Rasha kafin su biya diyya ga ma'aikata 'yan ci-rani."
Tun lokacin da aka dora wa yankin na Sochi nauyin karbar bakoncin gasar ta Olympics a shekarar 2007, mahawara ta yi zafi game da keta hakkin dan Adam a China wadda ta shirya wasannin Olympics na lokacin bazara a Beijing, shekarar 2008. Kuma kwamitin IOC ya dauki alkawarin duba wannan batu, inji Janna Sauerteig ta kungiyar Amnesty International.
"A dangane da wasannin Olympics a China, kwamitin IOC ya yi ta jaddada cewa za a inganta batun kare hakkin dan Adam. Sai dai hakan bai faru ba. Ikirarin da kwamitin na IOC ya yi cewa wasannin Olympics a Rasha za su kai ga inganta batun kare hakkin dan Adam, a gaskiya har yanzu ba mu gani a kasa ba."
Wasanni, hakkin dan Adam da siyasa
A wani babban taro da ya gudana a Sochi kwanaki uku gabanin bude wasannin, shugaban IOC Thomas Bach ya nuna matukar adawa da ko wane irin nau'i na wariya in da ya ce gwamnatin Rasha ta gina wata gada ta zinari, sun kuma gamsu da tabbacin da gwamnatin ta Rasha ta bayar cewa za ta mutunta ka'idojin Olympics a lokacin wasannin. Ya kuma yi kira ga siyasa na kasa da kasa da ka da su dora wa 'yan wasa nauyin sukar lamirin mai daukar bakoncin wasannin.
Shi ma wakilin Majalisar Dinkin Duniya a fagen wasanni motsa jiki Willi Lemke na ganin mahawarar tamkar wani karin nauyi ne ga masu shirya wasannin Olympics.
"Idan ka dubi wannan al'amarin to ke nan nan gaba ba za a samu wani birnin ko wata kasa da za a iya shirya gasar Olympics a ciki ba. Ba za a iya hana Amirka daukar nauyin wani wasa ba saboda jihohi 37 a kasar suna aiwatar da hukunci kisa."
Mawallafa: Mirjam Gehrke / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Pinado Abdu-Waba