1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

Gasar Euro 2024: Wasannin quater finals

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim LMJ
July 3, 2024

An kammala daukacin wasannin zagaye na 'yan 16 wato mataki na biyu a gasar neman lashe kofin kwallon kafa na kasashen nahiyar Turai da ke gudana a nan Jamus.

Euro 2024 | Quater Finals | Turkiyya | Nasara
Turkiyya ta yi nasarar kai wa zagayen quater finals a gasar Euro 2024 da ake yi a JamusHoto: Matthias Koch/IMAGO

A kwai dai darussa da dama a wannan mataki da aka kammala na zagayen 'yan 16, inda a wasannin da aka fafata ranar Talata Turkiyya ta doke Austriya da ci biyu da nema. Mai tsaron baya na Turkiyyan Merih Demiral ne ya zura duka kwallayen biyu rigis da suka bai wa Ankarar nasarar korar Austria daga gasar ta bana. Ita kuwa Holland ta casa Romania da ci uku da nema, godiya ga Donyell Malen da ya zura kwallaye 2 cikin ukun da kuma Coady Gakpo da ya zura kwallo daya. Ranar Jumma'a da ke tafe biyar ga wannan wata na Yuli da muke ciki, za a fara wasannin zagayen dab da na kusa da na karshe wato quater finals, kafin ranakun tara da 10 ga watan na Yuli a buga wasannin semi finals bayan an yi tankade da rairaya tsakanin kasashen da suka kai matakin na quater finals.

Karin Bayani: Faransa ta tsallaka zuwa quarterfinals a gasar Euro 2024

Spainiya za ta kece raini da Jamus mai masaukin baki da misalin karfe shida agogon Jamus din wato karfe biyar agogon Najeriya da da Nijar da Kamaru da Chadi, karfe hudu ke nan agogon GMT da Ghana. Za kuma a fafata tsakanin Portugal da Faransa da misalin karfe tara agogon Jamus wato karfe takwas agogon Najeriya da da Nijar da Kamaru da Chadi, kana karfe bakwai agogon GMT da Ghana. A Asabar din karshen mako kuwa, Ingila za ta fafata da Switzerland da misalin karfe biyar agogon Najeriya da da Nijar da Kamaru da Chadi, karfe hudu ke nan agogon GMT da Ghana.  Za a buga wasan karshe a wannan zagaye tsakanin Holland da Turkiyya da misalin karfe takwas agogon Najeriya da da Nijar da Kamaru da Chadi, kana karfe bakwai agogon GMT da Ghana.

'Yan wasa uku ne ke kan gaba wajen zura kwallaye a gasar, wadanda ke da kwallaye uku kowannesu a yanzu haka. 'Yan wasan su ne Cody Gakpo na Holland da Jamal Musiala na Jamus da kuma Georges Mikautadze na Georgia da tuni aka fitar da kasarsa daga gasar, mai tsaron ragar kasar Portugal Diogo Costa ya sha yabo sosai kan kokarin ceto kasarsa da ya yi a lokacin bugun daga kai sai mai tsaron gida a zagaye na biyu da suka buga da Slovenia. Diogo Costa dai, ya kabe kwallaye uku ya hana su shiga raga kuma ana cikin wa'adin karin lokaci wato extra time ya ceci kasarsa bayan sun yi ido hudu da fitaccen dan wasan Austria Benjamin Sesko amma ya tare kwallon da mai tsaron baya Pepe ya yi kuskuren barinta. Sai dai har yanzu tsohon zakaran duniya Cristiano Ronaldo bai jefa kwallo ko daya ba, a duka wasannin da ya buga a wanna gasa ta bana.

Karin Bayani: Potugal ta sha da kyar a hannun Chek a gasar Euro 2024

Ita kuwa Faransa na shan suka kan rashin zura kwallaye da yawa a gasar ta bana duk kuwa da tarin fitattun 'yan wasa da take da su, kasancewar kwallo daya tak ta jefa da kanta da Kylian Mbappe ya zura a karawarsu da Poland a wasan rukuni da suka tashi kunnen doki daya da daya. Sauran kwallaye biyun da Faransa ta ci dai, duka sun fito ne daga bangaren abokan karawarsu da suka ci kansu wato own goal. Mai masaukin baki Jamus ba ta tsira daga masu suka ba, kasancewarta gogaggiya wajen karbar bakuncin wasannin duniya dabam-dabam. Ta sha suka dangane da wasanta da Denmark da aka buga a birnin Dortmund da ruwan sama da kuma iska mai karfi suka rinka janyo dakatar da shi a lokacin da ake tsaka da bugawa, sakamakon yanayin tsarin filin.