Wasu ƙarin jama'ar sun kamu da Ebola
August 13, 2014Talla
Sanarwar ta ƙungiyar ta ce mutane 56 suka mutu da cutar a cikin kwanaki biyun da suka wuce a yammancin Afirka.
Hukumar ta ce tun daga lokacin da anobar ta ɓarke a cikin watan Maris, kawo yanzu ta kashe mutane 1069 yayin da aka tabbatar da cewar wasu 1975 sun kamu da cutar. Sama da mutane dubu ɗaya suka mutu da cutar a cikin ƙasashen Liberia da Gini da Saliyio da kuma Najeriya yazuwa yanzu.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Suleiman Babayo