Wasu Falasdinawa sun kai farmaki Isra'ila
May 29, 2018Mayakan sakai a yankin Falasdinawa a Gaza sun harba makaman roka har sau 25 da sanyin safiyar Talatar nan zuwa yankin Isra'ila, kamar yadda mai magana da yawun sojan na Isra'ila ya tabbatar. Lamarin da ya sanya aka kunna jiniya ta gargadi a garuruwa da dama da ke a kusa da Zirin Gaza.
Babu dai labarin wanda ya samu rauni ko halaka ta sanadin harba makaman da suka nufi yankin kudanci a cewar sojan na Isra'ila.
Wannan dai shi ne karon farko da aka harba makaman roka a yankin na Isra'ila tun bayan da Falasdinawa suka fara zanga-zanga a Gaza a ranar 30 ga watan Maris. Wasu rahotanni da suka fita daga yankin Falasdinawan sun ce jiragen sojan Isra'ila sun kai farmaki ga yankuna da dama a Gaza, lamarin da ya sanya aka rika jin karar ababen fashewa. Mai magana da yawuun sojan na Isra'ila dai ya ki cewa komai a game da wannan zargi.