Wasu kasashen AES sun kauce wa taron tsaro na Abuja
August 26, 2025
Kasashen Burkina Faso da Mali ba su halarci babban taron manyan sojoji na nahiyar Afirka da Najeriya ta shirya a jiya Litinin, yayin da dangantaka tsakanin kasashen Sahel da ke karkashin mulkin soja da makwabtansu na Yammacin Afirka ke ci gaba da kasancewa cikin yanayi marar dadi.
Kasar Nijar ce kadai daga cikin kasashen kawancen AES ta halarci taron da aka gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya, inda Kanal Soumana Kalkoye ya wakilce ta.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana wannan taro a matsayin irin sa na farko da manyan hafoshin nahiyar Afirka suka hadu, inda aka samu halartar shugabannin soji daga Djibouti har zuwa Namibiya domin tattaunawa kan dabarun yaki na hadin gwiwa da kuma neman hanyoyin magance matsalolin tsaro na cikin gida a nahiyar.
Hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa matsalolin tsaro suna shafar dukkan kasashen Afirka ba tare da la'akari da iyaka ba, inda ya yi kira ga samar da tsarin hadin kai na tsaro da Afirka za ta jagoranta da kanta.