1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro a Santanbul don gano bakin zaren rikicin Siriya

Zulaiha Abubakar MNA
October 27, 2018

Shugabannin kasashen Jamus da Turkiyya da Faransa da kuma Rasha na ganawa a birnin Santanbul na kasar Turkiyya kan nemo hanyoyin maido da zaman lafiya a kasar Siriya.

Türkei Vierer-Gipfeltreffen in Istanbul Merkel und Erdogan
Hoto: Reuters/K. Ozer

Shugabannin da ke taron a birnin Santanbul na kasar Turkiyya, suna fuskantar kalubale na banbancin ra'ayi tsakaninsu game da makomar Shugaba Bashar Assad na Siriya.

Kasar Rasha na zaman mai marawa shugaba Assad baya, yayin da Turkiyya ke taimakon 'yan tawayen da ke son hambarar da gwamnatinsa.

A nata bangaren kasar Jamus kuwa na cikin kashasen Turai da ke Allah wadai da harin da ake ci gaba da kaiwa a yankunan da fararen hula suke zaune a kasar ta Siriya.