1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Mai ajiye kakin sojoji ke nufi?

Muhammad Bello L
September 9, 2024

Dakarun sojojin Najeriya 196 ne aka sanar da sun mika takardar barin aiki, sakamakon abin da suka bayyana da cin-hanci da rashawa da ke kara kamari a aikin soja da ma raguwar karsashin aikin.

Najeriya | Tsaro | Sojoji
Wasu sojojin Najeriya sun ajiye aikinsu, ko mai hakan ke nufi?Hoto: DW/F. Muvunyi

Ko da yake rundunar sojojin Najeriyar ta ce ba haka labarin ya ke ba, tare da cewar sojojin da ke barin aikin na cike da burin barin kasar domin fadawa aikin na soja a wadan su kasashe. A baya-bayan nan ne bayanai suka fita na cewar kananan sojoji masu yawa sun mika takardar barin aikin, duk kuwa da cewar lokacin barin aikinsu bai yi ba. Wasu Karin bayanai dai na nuna cewar, sojojin masu barin aikin sun cimma shawarar hakanne sakamakon katutun cin-hanci da rashawa da ke kara kazanta a aikin soja da kuma raguwar karsashin aikin na saudakar da kai gami da tabarbarewar tsaron lafiyar jama'a da dukiyoyinsu kana babu kykkyawan tsarin kawo karshen hakan tsawon shekaru.

Hira da Janar Christopher Musa

06:48

This browser does not support the video element.

Wani da ya bar aikin na soja lokacin nasa bai yi ba da kuma ya nemi sakaya sunan sa ya ce rashin gaskiya da kuma matsalar da ke tattare da duk wani yunkuri na gudanar da aikin kamar yadda ka yi rantsuwa cewar za ka kare kasa da alummar kasarka. A cewarsa in har zaka dauki wannan mataki, to ba za ka shirya da manyanka ba saboda cin-hanci da rashawa. Ya ce sojojin na da shirin su yi aiki yadda ya kamata, amma ba a ba su makamai da harsasai ba isassu hakan ya sa 'yan bindiga su kan yi wa sojoji kawanya. Ya yi zargin cewa manyansu ba sa son matsalar tsaron ta kare, saboda makudan kudin da ke cikin harkar kana ba a bai wa sojoji hakkokinsu kamar yadda ya kamata. An dai nunar da cewa sojojin da ke shirin barin aikin na harin fadawa kasashen waje kamar Ukrain da Birtaniya da sauran kasashen da Ingila ta raina, domin neman aiki. Rundunar sojojin Najeriyar ta ce labarin ba haka ya ke ba, illa dai kawai da ma barin aikin soja shawara ce ta kashin kai.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani