Wata guda bayan harin ba zata na kungiyar Hamas a Isra'ila
November 7, 2023Isra'ila na ci gaba da luguden wuta a kan Zirin Gaza, wata guda bayan kazamin hari da mayakan kungiyar Hamas suka kaddamar wanda ya salwantar da rayukan sama da mutum dubu da 400 a Isra'ilar.
Hare-haren ramuwar gayya da dakarun Isra'ila suka kaddamar a kan Zirin Gaza dai ya halaka fararen hula sama da dubu 10 kawo i yanzu daga ciki akwai kananan yara dubu hudu, a cewar ma'aikatar lafiya ta yankin Falasdinu.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa za ta dauki alhakin halin tsaro na yankin Gaza har zuwa wani lokacin da bai fayyace ba bayan yakin.
Tuni dai babban jami'in hukumar kare hakkin bil Adama a Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk ya fara ziyarar kwanaki biyar a Gabas ta Tsakiya inda zai tattauna matsalolin da ake ciki da gwamnatoci gami da kungiyoyi a yankin.
Ko jiya Litinin ma dai Shugaba Joe Biden na Amurka ya tattauna da firaministan Isra'ila Mr. Netanyahu a kan yiwuwar samun saussauta hare-hare a Gazar saboda hali na jinkai.