1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wayar da kan jama'a a Nijar game da katin zabe

Larwana Malam Hami/ MNADecember 30, 2015

Kungiyoyin fararen hula a Jamhuriyar Nijar na kokarin fadakar da jama'a muhimmancin mallakar takardun zabe.

Niger Wahlen Politik Stimmen Auszählung
Hoto: DW/M. Kanta

A yayin da a Jamhuriyar Nijar lokacin zabukbuka ke kara karatowa, kungiyoyin fararen hula sun maida hankalinsu ga kiraye-kirayen jama'a na su tabatar da sun rike katunansu na zabe da zaran an fara rabawa. Wannan matakin da kungiyoyin fararen hular suka dauka na zama matakin farko na kauce wa masu zabe fadawa cikin matsalar cinkoson neman takardun zabe a ranar zabe, da hakan ke hana jama'a da dama sauke nauyin da ya rataya a kansu na kada kura'a a yayin zaben.


Wannan yunkuri na kungiyoyin fararen hular masu zaman kansu dai ya zo ne a daidai lokacin da tawagar kwararru daga kungiyar kasashen da ke amfani da
harshen Faransanci ta OIF ke sa ido a aikin binciken rijistar sunayen masu zabe a kasar ta Nijar.

Muhimmancin mallakar katin zabe ga dan kasa

Tun a zabubukan baya ma dai 'yan farar hular sun lura da cewar sai a ranaikun zabe ne jama'a ke kara kaina wajen neman takardun zabe kamar yadda Iliya Dan Malam na MPCR ta Nuhu Arzika ke cewa.

"Harkar zabe a kasashe masu tasowa irinsu Nijar za ka tarar wani ba ruwanshi da yin zaben saboda watakila ya taba yi amma bai samu gamsuwa ba. A yanzu dai muna kira ga kowa da ya nemi katinshi na zabe ya rike a hannunshi saboda ya ba da ra'ayinshi idan lokacin zabe ya zo. Muna waye ma mutane kai muhimmancin zabe da mallakar katin zaben, saboda sai da shi ne za a kada kuri'a kuma ita kada kuri'a wajabi ne ga dukkan dan kasa wanda ya dace."

Haka su ma dai kungiyoyin malaman makaranta da ke da ta cewa a cikin lamarin zabe idan aka dubi mahimmancinsa ta fuskar ci gaban rayuwar al'umma a cikin tafarki na dimokaradiyya inji Amadu Dan Kori daga hadaddiyar kungiyar malaman makarantun Sakandare tuni suka fara hannunka mai sanda ga jama'a.

Da ma dai 'yan adawa sun yi ta kira da wayar wa da jama'a kai a kan zabeHoto: DW/M. Kanta

"Harkar zabe abu ne da yake ya wajabta kan kowane dan kasa wanda ya cancanci kada kuri'a. Saboda a bangarenmu na kungiyoyin malaman makaranta muna wayar wa da mutane kai game da muhammancin zabe a matsayin wani nauyi da ya rataya kan kowane dan kasa."

Da sauran aiki ga 'yan kasa su san muhamminci zabe

To amman a cewar Maman Yahaya daga kungiyar tsoffin sojoji masu ritaya matakin da 'yan farar hular suka dauka ya yi dai-dai, sai dai bun takaici har yanzu sanin mahimmncin kuri'a ga dan Nijar da sauran zomo a kaba, ba kamar yadda su 'yan mazan jiya suka sani ba.

"Ya kamata da dan siyasa da gweamnati kowa ya zo ya ba da tasa gudunmawa wajen zabe. Ko yana da hakin kuri'a amma dan Nijar bai san hakinsa na kuri'a ba. Idan sun san matsayin 'yanci da matsayin doka da sun yi rige-rigen zuwa karbar katin zabe."

Matakin fadakar da mutanen dai na mallakar katin zabe na ci gaba da samun yabo da goyon bayan jama'a.