1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus: Kariya ga mazauna karkara

March 24, 2020

Sarakunan gargajiya a birnin Gaya na Jamhuriyar Nijar, sun dauki matakan wayar da kan al'ummomin da ke zaune a yankunan karkara kan matakan kariya ga annobar cutar Coronavirus ko COVID-19.

Symbolbild Hände waschen
Wanke hannu na daga cikin matakan kare kai da ma rage yaduwar cututtukaHoto: Imago Images/M. Westermann

Galibin al'umma mazauna yankunan karkara dai ba su da masaniya kan dokokin da gwamnati a  Jamhuriyar Nijar ta gindaya dangane da matakan kariya kan wannan cuta, hakan ya sa sarakunan gargajiyar daukar matakin fara fadakar da al'umma mazauna kauyukan da ke karkashinsu kan yadda ya kamata su bi dokokin domin kare kansu da ma sauran mutane.

Hukumomin a da'irar birnin Gayan da kuma sarakunan gargajiyar dai sun tattauna da masu jiragen ruwa da masu sa'nar kabu-kabu domin yi musu gargadi kan bin dokar da kuma kiyayewa da bin hanyoyin ratse na bayan fage don shiga ko fita zuwa cikin wasu kasashe. A wasu unguwanin dai tuni a ka fara tayar da jijiyoyin wuya tsakanin malamai da kuma jami'an tsaro a kan batun yin salla a Masallatai. Daga bangaren masu sana'ar kabu-kabu dai tuni uwar kungiyarsu ta soma daukar matakai na ganin 'ya'yanta sun bi dokar sau da kafa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani