Darfur: WFP ta dakatar da aikinta
December 31, 2021Talla
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce an kai hari tare da kwasar ganima a wuraren aje kayayyakinta uku tare da yin kiyasin yashe mata tan 500 na kayayyakin abinci. A makon da ya gabata ne wata kungiyar masu tada kayar ta kai harin, lamarin da ya haifar da sanya dokar takaita zirga-zirga a lardin, sai dai kuma hakan bai razana barayin ba.
Hukumar ta kuma ce ba zata iya karkatar da tallafinta ga sauran sassan gabashin nahiyar Afirka ba tare da ta cimma bukatun marasa galihu a Sudan ba. Sudan na daga cikin jerin kasashe matalauta a duniya, inda kimanin mutane miliyan 11 suke rayuwa cikin halin matsi da yunwa.