1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WFP ya dakatar da aikinsa a arewacin Yemen

Abdullahi Tanko Bala
January 29, 2026

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya dakatar da ayyukansa a arewacin Yemen mai fama da rikici

Shirin samar da abinci na MDD a Yemen
Shirin samar da abinci na MDD a YemenHoto: Khaled Ziad/AFP/Getty Images

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya dakatar da ayyukansa tare da sallamar ma'aikatansa a yankin arewacin Yemen da ke hannun yan tawaye sakamakon tarnaki da cin zarafi da yan tawayen Houthi ke yi wa jami'an hukumar.

Shirin samar da abincin ya fara ne da jingine ayyukansa a watan Augusta a yankin yan Houthin da ke fama da rikici fiye da shekaru goma da suka wuce.

Akwai yiwuwar matakin zai kara ta'azzara halin tagaiyarar al'umma a kasar ta Larabawa da ke fama da yakin basasa tun 2014.

A cewar jami'an Majalisar Dinkin Duniya, dakatar da ayyukan zai shafi ma'aikata 365 na shirin abincin na MDD da suka rage a arewacin Yemen wadanda za su rasa aikin su daga nan zuwa karshen watan Maris.