An sami 90% na ingancin maganin corona
November 9, 2020Wani babban jami'in hukumar lafiyar ta duniya Bruce Aylward da ya sanar da hakan ya ce samun maganin zai sauya yadda cutar ke yaduwa.
A waje guda kamfanin hada magunguna na Jamus BioNTech tare da hadin gwiwa da kamfanin Pfizer na Amirka sun sanar da cewa sun sami ingancin kashi 90 cikin 100 na allurar da suka samar bayan gwajin ingancin maganin har sau uku.
Sanarwar da kamfanonin biyu suka bayar shi ne sakamakon nasara ta farko na bayanai da aka samu daga gagarumin gwajin allurar rigakafin cutar ta corona.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya wallafa a shafinsa na Twitter yana maraba da samun maganin wanda ya ce abin karfafa gwiwa ne.
Ya kuma jinjinawa masana kimiyya da sauran abokan hulda a sassan duniya wadanda ke kokarin samar da magani mai inganci na yaki da cutar Covid-19.