WHO: Intanet na sa bazuwar cututtuka ta jima'i
June 7, 2019Talla
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana irin koma bayan da ake fuskanta ta fuskar yaki da cututtukan da ke yaduwa ta hanyar jima'i, tana mai gargadi kan karuwar manhajojin da ke kitsa hulda tsakanin maza da mata a shafukan Intanet.
Sama da mutum miliyan guda ne ke kamuwa da cutukan na jima'i a kowace rana a duniya, inda ake samun akalla mutum guda cikin mutum 25 da ke kamuwa da wani nau'i na cutar.
Ta nuna damuwa da yadda mutane suka mayar da jima'i a rayuwar yau, da ma ake iya samu a sawwake ta hanyoyin na Intanet.
Hukumar ta dai danganta yin watsi da matakan kariya da masu dabi'ar ke yi da kasancewa cikin dalilian karuwar matsalar a fadin duniya.