1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Kasashe za su rabu da Maleriya

Yusuf BalaApril 25, 2016

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fitar da wani tsari daga shekarar 2016 zuwa 2030 na ganin ta kawar da cutar Maleriya a cikin akalla kasashe 10 wanda wasunsu na Afirka ne.

Zika Virus WHO Margaret Chan
Margaret Chan babbar darakta a WHOHoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

Kasashen Afirka shida ne za su yi ban kwana da cutar Maleriya nan da shekarar 2020 kamar yadda rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya nunar a ranar Litinin din nan, rahoton da ke fita a wani bangare na bikin ranar Maleriya ta duniya.

A cewar hukumar kasashe 21 ne ke da alamu na iya kawar da cutar ciki kuwa har da shida daga nahiyar Afirka.Wadannan kasashe kuwa su ne Aljeriya da Baswana da Cape Verde da Kwamaras da Afirka ta Kudu da Siwaziland.