WHO: Bukatar kawar da maganin jabu
January 24, 2023Talla
Kungiyar lafiya ta duniya WHO ta bukaci daukar matakan gaggawa domin kawar da gurbatattun magungunan da aka danganta da mace-macen daruruwan yara a Afirka da nahiyar Asiya.
Yara fiye da 300 ne suka rasu sakamakon gurbataccen maganin tari a kasashen Gambiya da Uzbekistan da Indonesia a shekarar 2022.
Da dama daga cikin yaran basu wuce shekaru biyar da haihuwa ba.
Ana kyautata zaton lamarin yana da dangantaka da gurbataccen maganin tari da aka yi a Indiya da Indonesiya da wasu sinadarai masu matukar hadari.