1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

WHO na neman a kwashe mutane daga asibitin al-Shifa na Gaza

Mouhamadou Awal Balarabe
November 19, 2023

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi tir da fadada hare-haren da isra'ila ta yi a asibitin al-Shifa wanda shi ne mafi girma a zirin Gaza, inda ta bukaci a kwashe marasa lafiya saboda ya zama "yankin mutuwa".

Duban Falasdinawa ne ke kwance a asibitin al-Shifa bayan samun rauni
Duban Falasdinawa ne ke kwance a asibitin al-Shifa bayan samun rauniHoto: Khader Al Zanoun/AFP

A yayin da aka shiga kwana na 44 na sabon rikicin a yankin Gabas ta Tsakiya, sojojin Isra'ila na ci gaba da fadada ayyukansu a wasu sabbin yankuna na zirin Gaza, inda suka kai farmaki a yankunan Jabaliya da Zaytoun a arewacin yankin. Kungiyar Médecins Sans Frontières (MSF) ta sanar da cewa daya daga cikin ma'aikatanta ya rasa wani danginsa daya yayin da wani karin daya ya jikkata lokacin da aka kai hari kan ayarin motocin da ke kwashe mutane 137 daga al-Shifa. Amma MSF ba ta fayyace asalin wadanda suka yi harbe-harben ba.   

Karin bayani: Matsayar Jamus a rikicin Isra'ila da Hamas

Ita kuwa Hamas da wasu kasashen Yamma ke dauka a matsayin kungiyar ta'addanci ta bayyana cewar hare-haren da Isra'ila ta kai a sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya sun yi sanadin mutuwar mutane fiye da 80, ciki har da akalla 50 a makarantar da aka tsugunar da wasu Falasdinawa. sai dai rundunar sojojin Isra'ila ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa "ta samu rahoton lamarin, amma tana bincike kan zaharin abin da ya faru.

Karin bayani: Netanyahu na shan suka a cikin gida

Fadar mulki ta White House ta Amurka ta ce tana ci gaba da aiki tukuru domin cimma yarjejeniya tsakanin Isra'ila da Hamas kan mutanen da aka yi garkuwa da su. Sannan shugaban Amurka Joe Biden ya yi barazanar haramta bizar zuwa Amurka ga Yahudawa da ke da tsattsauran ra'ayi da ke kai hari kan fararen hula a Yammacin Kogin Jordan.