SiyasaAfirka
WHO ta ce babu sauran gurbataccen maganin tari a Afirka
April 22, 2024Talla
A farkon Afrilun 2024 atan Najeriya ta janye maganin tarin yara da ta samu na dauke da sinadarin toxin da yawansa ya wuce misali.
Karin bayani: Hanyoyin inganta lafiya a Afirka
Suma wasu kasashen Afirka 5 da suka hada da Kenya da Rwanda da Tanzaniya da Zimbabwe da Afirka ta Kudu inda aka sarrafa shi sun janye maganin daga shaguna bayan samunsa da illa ga yara.
Karin bayani: Lafiya Jari: Illar Aspartame
Kamfanin Johnson & Johnson ne dai ya sarrafa maganin na Benylyn a watan Mayun 2021 a Afirka ta Kudu ko da yake a yanzu kamfanin Kenvue ne mallakinsa tun bayan raba gari da J&J din.