Lafiya
Iran: WHO ta dakatar da babbar cibiyarta a Dubai
March 5, 2026
Talla
Shugaban hukumar Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a wannan Alhamis cewa dakatarwar ba ta shafi kasashen da abin ya faru kusa da su kawai ba, domin cibiyar na taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa harkokin lafiya na gaggawa a duniya baki daya.
Karin bayani: Tasirin yakin Iran kan alakarta da Afirka
Daraktar WHO mai kula da yankin Gabashin Bahar Rum, Hanan Balkhy, ta ce cibiyar Dubai ta kula da rarraba kayan agajin gaggawa guda 500 da aka aika zuwa kasashe 75 a shekarar da ta gabata.
Ta kara da cewa rikicin da ke faruwa yanzu ya hana kaiwa ga kayan tallafin lafiya na kusan dala miliyan 18, yayin da wasu kaya na darajar dala miliyan 8 ma ba su iya isa cibiyar ba.