1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

WHO: Turai na jinkirin samar da rigakafin corona

April 1, 2021

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta soki tsarin aiwatar da ringakafin corona a nahiyar Turai, tana mai suffanta lamarin da wani abu mai kama da tafiyar-hawainiya.

WHO Europa Hans Kluge
Hoto: Alberto Pizzoli/AFP/Getty Images

WHO ta ce rashin ba da kulawar da ta kamata da hukumomi a Turai ke yi wa shirin rigakafin coronar na haifar da karin zullumin bunkasar sabon samfurin corona da ke naso a Turai.

Daraktan WHO a nahiyar Turai Hans Kluge ya ce jinkirin da ake samu a wurin rigakafin na tsawaita rayuwar corona a Turai. A cikin wata sanarwa da jami'in na WHO ya fitar ya ce samar da rigakafi ita ce kyakkyawar hanyar kawar da corona, a don haka wajibi ne Turai ta kara kaimi wurin samar da rigakafin, sannan ta tabbatar rigakafin na kaiwa ga mutane ba tare da jinkiri ba.