WHO: Kakkabe cutar Polio a Najeriya
August 25, 2020Talla
Wannan mataki na zuwa ne bayan da hukumar ta ce an share sama da shekaru hudu ba tare da an sami cutar Polio a Najeriya ba, kasancewarta kasa ta karshe da ta yi ta fama da cutar.
A sanarwar da shugaban Hukumar ta lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya fitar, ya nuna godiya ga jami'an gwamnati da ma'aikatan lafiya da kuma masu bada gudumawa akan irin rawar da suka taka na kawo karshen cutar.