1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

WHO za ta kawo na'urorin gwajin Covid-19 a Afirka

September 29, 2020

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta sanar da shirin tallafa wa kasashe masu raunin tattalin arziki da na'urorin gwajin coronavirus.

Tedros Adhanom Ghebreyesus, Direktor WHO
Hoto: picture-alliance/dpa/KEYSTONE/S. D. Nolfi

Hukumar tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi sun ce za su raba na'urorin gwaji guda miliyan 120 ga irin wadannan kasashe. 

Shugaban Hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce kasashe 20 na Afirka na cikin wadanda za su samu wadannan na'urori da ke bayar da sakamakon gwajin corona a cikin mintuna 15 zuwa 30 a maimakon kwanaki da wasu na'urorin gwajin coronon ke dauka kafin su fitar da sakamako.

A watan gobe na Oktoba ne dai ake sa ran hukumar za ta kaddamar da wannan shiri. Sai dai kawo yanzu WHO ta ce ba ta kammala samun Dala miliyan 600 da shirin ke bukata ba.