WHO za ta wuce wa'adin da ta diba dan yaki da Ebola
December 1, 2014Watanni biyu da suka gabata ne hukumar ta WHO ta gabatar da wani shiri mai dogon buri, wannan shirin dai, ya kunshi kebe akalla kashi 70 cikin 100 na wadanda suka kamu da wannan cuta, da kuma binne gawawwakin kashi 70 na wadanda suka rasu sakamakon cutar, bisa irin tanadin da ya dace, a kasashen da suka fi fama da radadin cutar wato Guinea Liberiya da kuma Saliyo, kafin ranar daya ga watan Disemba.
To sai dai, yau ne wannan wa'adin ke cika, kuma bisa bayanan hukumar, kasar Guinea ce kadai ta ke kan hanya ganin a Liberia kashi 23 na wadanda suka kamu da cutar ne, aka iya kebewa, a yayin da ake cigaba da fuskantar tsaiko wajen samun jami'an da za su kawar da gawawwakin wadanda suka rasu. Lamarin da ke tabbatar da cewa hukumar ta WHO, za ta wuce wannan wa'adi ba tare da ta cimma burin nata ba.
Ko da yake a nata bangaren hukumar ta ce a 'yan makonnin baya-bayan nan, an sami nasarar rage yaduwar cutar a kasashen Guinea da Liberiya sai dai kasar Saliyo inda har yanzu ake samun karuwar adadin masu cutar a babban birnin kasar dama kewaye.