1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mai yiwuwa Jemage ne silar corona - WHO

Abdul-raheem Hassan
March 29, 2021

Rahoton kwararru a fannin lafiya da suka je binciken silar cutar corona a Wuhan, na cewa akwai yiwuwar Jemage ne ya fara yada cutar ga bil Adama ta hanyar wasu dabbobin cikin gida.

Flying Foxes
Hoto: M. Woike/blickwinkel/picture alliance

Wani babin binciken da kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP ya samo gabannin sake rahoton a hukumamnce, na kara nuna shakku kan camfin cewa cutar ta kubuce ne daga dakin gwaji .

Bincike da ya samu hadin gwiwar kwararru daga hukumar lafiya ta duniya da na kasar China, na shirin fita ne a lokacin da wani sabon nau'in cutar ke tilasta kasashen Turai tsaurara matakan yanki da annobar.