1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WTO: A wadata duniya da rigakafin corona

May 6, 2021

Kungiyar Kasuwanci ta Duniya WTO karkashin shugabarta Ngozi Okonjo-Iweala ta bukaci ganin an yi raba daidai wajen samar da rigakafin annobar COVID-19 a duniya baki daya.

Ngozi Okonjo-Iweala | neue WTO-Chefin
Hoto: Gian Ehrenzeller/KEYSTONE/dpa/picture alliance

Sabuwar shugabar kungiyar kasuwanci ta duniya WTO Ngozi Okonjo-Iweala ta yi kira da a hau teburin tattaunawa domin tsara yadda za a wadata kasashen duniya da alluran rigakafin COVID-19 ba tare da nuna fifiko ko wariya ba. Shugabar ta yi wannan kiran ne a wajen babban taron kungiyar, inda ta ce ta haka ne kawai za a iya yakar cutar bai daya domin a gudu tare a kuma tsira tare.

Batun na wadata duniya da rigakafin da alama ya samu karbuwa a wajen taron, bayan da wakilan kasashe arba'in mambobin kungiyar WTO da suka gudanar da jawabai, sun kara da cewa baya ga samun wadatar rigakafin, ya kuma cancanta a kara ingancinta tare da rarraba ta  lunguna da sakuna na fadin duniya.