1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko 'yan Afirka za su shugabanci WTO?

July 8, 2020

Daga cikin wadanda aka gabatar da sunayensu domin neman mukamin shugabancin kungiyar Kasuwanci ta Duniyar daga Afirka dai, akwai Ngozi Okonjo-Iweala tsohuwar ministar kudi a Tarayyar Najeriya.

Bildkombo | Ngozi Okonjo-Iweala und  Amina Mohamed
Matan Afirka da ke neman shugabancin WTO. Ngozi Okonjo-Iweala da Amina Mohamed

Baya ga mukamin ministar kudi da ta rike har sau biyu dai, Ngozi Okonjo-Iweala ta kuma rike ministar harkokin kasashen ketare ta Najeriyar. A karshen watan Agusta mai zuwa ne dai shugaba mai ci Roberto Azevêdo dan kasar Brazil zai yi ritaya. Ana dai zaben shugaban kungiyar ne ta hanyar tattaunawa a tsakanin kasashe. Sai dai a wannan karon da alama fafatawar za ta yi zafi har ta kai ga jefa kuri'a.

Lokacin Afirka ya yi?

Afirka dai ba ta taba samun wani danta da ya jagoranci kungiyar Kasuwancin ta Duniya wato WTO ba. Sai dai a wannan karon tsohuwar ministar kudin ta Najeriya  Okonjo-Iweala ta shiga sahun mutane shida da ke son a ba su damar jagorantar wannna babbar kujera mai matukar daraja ga tattalin arzikin duniya. Alhaji Shu'aibu Mikati masanin tattalin arziki ne a Najeriya, kuma a cewarsa Ngozi Okonjo-Iweala ta cancanci jagorantar kungiyar Kasuwancin ta Duniya wato WTO.

Ofishin kungiyar Kasuwanci ta Duniya WTOHoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

To sai dai duk da wannan ra'ayi na Alhaji Shu'aibu Mikati tsohuwar ministar kudi da harkokin kasashen waje ta Najeriyar dole ne ta shawo kan wasu 'yan uwanta 'yan Afirka guda biyu da suka nuna sha'awar tsayawa takarar neman kujerar. Mutanen kuwa su ne  tsohuwar ministar harkokin wajen kasar Kenya Amina Mohammed da kuma Hamid Mamdouh kwarare a kan harkokin jakadanci na kasar Masar. Sai dai kuma kawo yanzu wadannan mutane ba su nuna alamun za su janye su bar wa Okonjo-Iweala takarar shugabancin WTO din ba.

Tarin kalubale ga sabon shugaba

Amma duk da haka Dr Ebo Turkson mai sharhi a kan tattalin arziki na cewa idan dan Afirka ya samu wannan kujera to duniya za ta amfana: "Ni a ganina idan har wani daga cikinsu ya samu dama zai kawo sauyi sosai, domin dukkaninsu suna da kwarewa, idan aka duba mukaman da suka rike a baya. A saboda haka wadannan 'yan Afirka za su samu damar ciyar da duk wata tattaunawar da kungiyar WTO ta fara yi da wasu hukumomi a kan kasuwanci."

Dan jarida Liam Fox na BirtaniyaHoto: picture-alliance/empics/PA Wire

A yanzu dai ko kasashen Afirkan sun janye su bar wa daya ko ma ba su yi ba, 'yan takara daga Afirkan da ke zawarcin kujerar shugabancin WTO din za su fuskanci kalubale daga kasar Koriya ta Kudu, wacce ta gabatar da  Yoo Myung-he  domin ya dare kujerar. Kasashen Mexico da Maldoba su ma sun gabatar da na su 'yan takarar, yayin da Birtaniya  ta mika sunan kwararren dan jarida Liam Fox domin a ba shi wannan kujera. Ya kuma yi karin haske a kan abin da ya ke fatan yi idan ya samu wannan dama. "Kowa zai ci gajiya idan muka tabbatar da cewa kasuwanci na tafiya ba tare da jinkiri ko wata tangarta ba. Duk abin da wani daga waje zai ce, burinmu shi ne mu ga an samu sakamako wanda zai amfani kowa a wannan wuri."

Duk mutumin da ya yi nasara aka nada shi shugaban kungiyar Kasuwancin ta Duniya wato WTO, zai fuskanci gagarumin kalubalen dawo da alakar kasuwanci wacce ta yi tsami a tsakanin Amirka da Chaina. Kazalika dole ne sai sabon shugaban kungiyar ta WTO ya ci karo da kalubalen da coronavirus ke ci gaba da haifarwa ga tattalin arzikin duniya.