1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKoriya ta Kudu

Wutar daji ta halaka mutum 18 a Koriya ta Kudu

March 26, 2025

Gobarar ita ce mafi muni cikin gomman shekaru, sannan ta tilasta wa sama da mutane 27,000 tserewa daga muhallansu.

Gobarar ta tilasta wa mutane sama da 27,000 kaura daga muhallansu
Gobarar ta tilasta wa mutane sama da 27,000 kaura daga muhallansuHoto: Yasuyoshi Chiba/AFP/Getty Images

Akalla mutum 18 ne suka rasu a wata gobarar daji mai muni da ta auku a tarihin Koriya ta Kudu baya ga mummunar barna da ta haddasa.

Mukaddashin shugaban kasar ya sanar a ranar Laraba cewa wutar dajin ta rabu kashi daban-daban har fiye da goma tun karshen mako inda ta lakume wasu yankunan kudu maso gabashin kasar.

Ana shari'ar karshe ta makomar tsige Yoon Suk Yeol

Har ila yau, ta kuma tilasta wa kusan mutum 27,000 kaurar gaggawa bayan ta datse tituna da kuma na'urorin sadarwa kamar yadda mazauna yankunan da ke neman tsira da rayukansu suka sanar.

Wani jami'in Ma'aikatar Kare Mutane ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutum 18 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon wutar dajin baya ga wadanda suka jikkata.

Blinken na ziyara a Koriya ta Kudu

A wani batun da ya shafi kokarin kashe wutar kuma wani jirgin sojin Koriya ta Kudun mai saukar ungulu ya fadi da safiyar nan inda matukinsa ya rasu a kokarin dakile gobarar mai haddasa barna.