1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abubuwa biyar game da Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
November 27, 2025

Fitaccen malamin addinin Muslunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya jima yana da'awar addinin bisa tafarkin darikar Tijjaniyya, kuma ya yi suna wajen yin tafsirin al-Qur'ani.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Sheikh Dahiru Usman BauchiHoto: DW

Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa, bayan da ya shafe shekaru 101 a duniya.

An haife Sheikh Dahiru Usman Bauchi a garin Nafada, da ke cikin jihar Bauchi, amma yanzu tana karkashin jihar Gombe ne a ranar biyu ga watan Muharram na shekara ta 1346 bayan hijirar Muhammad SAW, abin da ya sa a lissafin Musulumci ya cika shekaru 100 a duniya. Koda yake a lissafin shekarar miladiyya an haife shi ne a shekara ta 1927.

Wane ne Dahiru Usman Bauchi?

Tarihi ya nunar da cewa shehin malamin na da shekaru 10 a duniya ya haddace al-Qur'ani, sannan yana da shekaru 20 ya fara karantarwa da hidima ta da'awa na kimanin shekaru 80, kana yana da 'ya'ya mahaddata akalla 73 da kuma jikoki sama da 200.

Sheikh Dahiru Bauchi yana daya daga cikin manyan shugabannin addini a arewacin Najeriya, kuma daya daga cikin shugabannin darikar Tijjaniyya, ya taimaka wajen yada ilimin addini, karfafa zaman lafiya, da hadin kai tsakanin Musulmi.

Sheikh Dahiru Bauchi ya shahara a fannin tafsirin Qur'ani wanda ya shafe fiye da shekaru 50 yana gudanarwa a Najeriya. Wannan tafsiri ya taimaka wajen kara fahimtar Musulunci a tsakanin jama'a, ilmantar da dubban mutane a cikin harshen Hausa, da yada ilimin Qur’ani ga matasa da manya.

Yadda Sheikh Bauchi ya yi wa addinin Musulunci hidima

Wane ne Sheikh Darhiru Bauchi?

This browser does not support the audio element.

Ya kafa makarantu da dama, musamman tsangayu, inda aka horar da dubban almajirai da malamai, kuma wasu daga cikin almajiransa sun zama manyan malamai a Najeriya da kasashen Afrika.

 Shehin ya kasance daya daga cikin shugabannin da ke amfani da iliminsu wajen sasanta rikice-rikice na addini da faɗakar da jama'a kan zaman lafiya da karfafa hadin kan Musulmai.

Da'awar darikar Tijjaniyya cikin natsuwa da hikima

Sheikh Dahiru Bauchi yana cikin fitattun jagororin Tijjaniyya a Najeriya, ya kuma yi aiki tukuru wajen koyar da bin sunnah ta Muhammad SAW bisa koyarwa ta darikar Tijjaniyya, ya kuma yi kokari tukuru wajen gyara kura-kuren da ake yawan dangantawa da darikar, ta hanyar wa'azi da tarukan tafsirai ga jama'a da hadin kai tsakanin mabiya a lokuta da dama.

 Sheikh Dahiru Usman Bauchi, yana bayyana matsayinsa a bainar jama'a kan abubwa da dama kamar cin zarafin Musulmai da siyasa da addini a cikin siga ta natsuwa ba tare da tashin hankali ba, sannan kuma mariganyin ya ilmantar da matasa tare da kwadaita msusu neman ilimin addini.

Dahiru Bauchi 100. Geburtstag - MP3-Stereo

This browser does not support the audio element.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi yana daga cikin manyan malaman da ke fassara al-Qur'ani da ayoyin al-Qur'ani a yayin taffsiran da ya sha gudanarwa a Najeriya. Yana karbar baki da ke tururuwa zuwa zawiyarsa a Bauchi, ciki har da fitattun 'yan siyasa daga ciki da wajen Najeriya da sarakunan gargajiya da malamai na darikar Tijjaniyya da ma wasu darikun na daban, da mabiya daga sassan yankunan da yake da'awa na Najeriya da kasashen Afirka.  

A ranar Juma'a (28.11.2025) ne ake gudanar da jana'izar marigayin karkashin jagorancin Sheikh Sharif Sharif Saleh.