China ta gargadi Trump kan batun Taiwan
May 14, 2026
Shugaban Kasar Chaina Xi Jinping ya gargadi takwaransa na Amurka Donald Trump kan cewa kasashen biyu na iya fadadawa cikin rikici, idan har Washington ta yi kuskure kan yadda take tafiyar da batun Taiwan.
Hankali ya koma kan ganawar Trump da Jinping
A yayin ganawar shugaban biyu a birnin Beijing, shugaba XI Jinping ya nanata cewa batun Taiwan shi ne mafi muhimmanci a dangantakar da ke tsakanin Chaina da Amurka, kuma inda aka tafiyar da lamarin cikin hikima kwanciyar hankali za ta dore a tsakanin kasashen biyu, yayin da kuskure ka iya haifarda sabani har ma ta kai ga fadawa rikici.
Sai dai a lokacin da yake wannan gargadi shugaban na Chaina ya yi amfani da wata kalma a cikin yaren Mandarin, da ba lallai ne tana nufin fadawa rikin soji kai tsaye ba.
Amurka ta bukaci China ta dakatar da yi wa Taiwan barazanar soji
A nasa bangare shugaba Donald Trump ya shaidawa Xi Jinping cewa akwai kyekkyawar makoma mai cike da nasara a dangantakar Amurka da Chaina, duk da sabani da takaddama da ke tsakanin manyan kasashen biyu a fannoniu daban-daban.