Shugaba Xi Jinping zai dore a wa'adi na uku a China
October 23, 2022Talla
Taron kolin jam'iyyar Kwamisancin a China ya zabi shugaban kasar Xi Jinping a wani sabon wa'adi na uku na shugabanci jam'iyyar, wanda hakan ka ba shi damar cigaba da tafiyar da harkokin mulki, abin da ke zaman na farko a tarihi.
Bayan Shugaba Jinping, taron ya kuma zabi wasu da ake ganin na hannun damansa hudu a mukamai mabanbanta don tafiyar da harkokin jam'iyyar da ma mulki. A cikin watan Maris na 2023 ake sa ran taron kwamitin zartarwar jam'iyyar Kwamisancin ya zabi Li Qiang shugaban Shanghai a matsayin sabon firaminista inda zai maye gurbin Li Keqiang.
Wasu da suka hada da Ding Xuexiang da Li Xi shugaban jam'iyyar a lardin Guangdong na daga cikion wadanda aka nada a manyan mukamai na tafiyar harkokin mulki.